Daga Zanji Sinkala
Zambia na ta fama da gwagwarmayar magance matsalolin tattalin arzikinta inda gwamnati ta tunkari Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF don karbar bashi.
Amma wasu ‘yan kasar ta Zambia da dama sun koka inda suka ce sharuddan da IMF suka saka wa kasar sun sanya su cikin wahalhalu.
Asusun na IMF a tsawon shekaru yana fuskantar rashin aminta da zubewar daraja a bangarori daban-daban na kasashe masu tasowa, saboda tasirin sharuddan bayar da bashi na sauyan fasalin manufofin kaashen.
IMF na cewa manufofi da sharuddansu sun daina rufe ido ga muhimman bukatun ‘yan kasa. Shin wannan hakan yake ko kuma kalaman siyasa na kawai?
A ‘yan shekarun nan dimbin basussukan humomi sun shake kasashe masu tasowa a kudancin duniya, musamman yadda aka fuskanci radadin Korona da kuma yakin Yukren.
A lokacin da suka matsu su fita daga kuncin da suka samu kawunansu a ciki, kasashe sun dinga zuwa wajen hukumomin kudi na kasa da kasa irin su IMF da karbar bashin kudade da suka baiwa sunan “Bailout” (Tallafin farfadowa) ko “Debt relief” (Bashin waraka).
Amma kuma, wannan bashi ba ya kawo wata waraka, face sake jefa kasashen cikin matsi da halin kaka ni ka yi. Sri Lanka na daya daga cikin misalan da za a iya bayarwa.
Kasar na fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni a shekara 70 da suka gabata, bayan ta gaza biyan bashin da ake bin ta a watan Mayun 2022.
Zambia ma ba a bar ta a baya ba wajen gaza biyan bashin da ake bin ta. A 2020 Zambiya ta zama kasar Afirka ta farko da ta da ta kasa biyan bashin kasashen waje da ya kai yawan dala biliyan 17.3.
A wannan lokacin, gwamnatin shugaba Edgar Lungu ta bukaci IMF da y aba su kudin farfadowa daga radadin Korona da rashin ruwan sama da kasar ta fuskanta.
A 2021, sabuwar gwamnatin kasar karkashin Hakainde Hichilema ta sanya hannu kan karbar bashin dala biliyan 1.3 daga hannun IMF.
Gwagwarmayar gyara
Amma wannan bashi na farfadowa na IMF, kamar ko yaushe ya zo da sharudda da suka hada da na kasha kudade – da ma janye tallafin man fetur, da sauya fasalin hasashen cigaban tattalin arzikin gwamnati – daga gibin kaso 6 zuwa rarar kaso 3.2 nan da 2025.
Wannan na afkuwa ne bayan shekaru 8 da Asusun na IMF ya bukaci gwamnatin Zambia da ta da bar kasha kudadenta a kaso 36 na kudin da take samu a cikin gida, sanna kar ta gaza kaso 8 na kudaden da take samu.
Hakan ya tankwara gwamnati wajen rage albashi sannan ta kara yawan wasu alawus-alawus na ma’aikata.
Sakamakon da ya biyo baya ya munana matuka, kuma ya janyi gazawar kungiyoyin malamai sun sasanta don neman ingantacce yanayin koyo da koyarwa da Karin albashi.
An yarda wannan ya ci karo da kokarin inganta ilimi da yanayin koyo da koyarwa.
“Wannan ne lokacin da malamai suke karbar albashin da bai taka kara ya karya basannan kuma aka shiga lokacin daina Karin albashi. Yanayi ne mai wahalar gaske”, in ji wani malamin makaranta a Lusaka wanda ya nemi a boye sunansa.
Ya fada wa TRT Afrika cewa “’Yan kasar Zambia na da iyalai da yawa da suke kula da su, muna gwagwarmayar gyara wannan yanayi. Ba iya haka kadai ba ma, karsashin zuwa aiki ma ya dakushe.”
Bashi mai cutarwa
Rueben Lifuka, wani mai rajin kyakkawan shugabanci ya ce dar-dar din da wasu ‘yan Zambiya ke yi ya zo ne sakamakon mummunan tasirin da bashin IMF ya janyo a baya ne.
Amma kuma a nasa bangaren tana ganin bai ma dace a ce gwamnatin Zambia ta ruga da gudu wajen IMF don ciyo bashi ba, saboda irin illarsa da aka gani.
Ya shaidawa TRT Afrika cewa “IMF ya yi gaggawar bayyana wannan a matsayin hanyar waraka.
Suna cewa gwamnatin Zambia ce ta shirya yadda za a karbin bashin, muna yarda ne kawai. Za mu iya tambayar abu daya zuwa biyu, amma dai wannan batu ne da za a warware a cikin gida.”
“Wasu kasashen na zuwa wajen IMF idan suna cikin mawuyacin hali, wadanda mashassharar durkushewar tattalin arziki ke damun su,” in ji Lifuk.
Mai rajin dabbaka kyakkayawan shugabancin ya kuma bayyana cewa dole kasashen da ke cin bashin IMF su kawo wasu sauye-sauye da za su matsantawa al’ummar da suke jagoranta.
A lokacin da Zambia ke jiran makomarta, masu nazari na cewa yana da muhimmanci ga mahukuntan kasar su dauki matakin daidaita al’amura tare da inganta tattalin arziki, sannan su kuma bayar da fifiko ga bukatun ‘yan kasa.