Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar da za ta bayar da dama a dinga bai wa daliban kasar bashi marar kudin ruwa a lokacin da suke karatu.
A wani sakon bidiyo da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar Femi Gbajabiamila ya wallafa a Twitter, an ga Shugaba Tinubu yana sanya hannu kan dokar.
Gbajabiamila, wanda shi ne ya dauki nauyin kudurin dokar a matsayinsa na shugaban majalisar wakilan kasar, ya ce "Ina cike da murna da Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar bai wa dalibai bashi.
Ni na dauki nauyin wannan kudurin doka wanda zai taimaka wa dalibai marasa galihu da kuma iyalai da ke neman damar karatu a manyan makarantu."
Daga bisani shugaban kasar ya wallafa sako a shafukansa na sada zumunta inda ya ce "A yau ina farin cikin sanya hannu kan dokar Samun Damar Karatun Gaba da Sakandare, wadda ta bai wa daliban da suka cancanta a duk fadin kasa damar samun bashi marar ruwa don ci gaba da karatunsu zuwa manyan makarantu.
Wannan doka za ta ba mu damar tabbatar da cewa kowanne dalibi da ya cancanta ya iya samun ilimi cikin rahusa kuma mai inganci, ko daga ina ya fito."
A ranar 25 ga watan Mayun 2023 ne kudurin dokar ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Wakilan kasar.
Kasashen duniya da dama na bai wa dalibai bashi marar ruwa, wanda suke biya bayan kammala karatunsu.