Daga Mazhun Idris
‘Yan Nijeriya sun shiga wani yanayi na tsadar man fetur, a lokacin da matakin da yunkurin sabuwar gwamnati na cire tallafin man fetur ya jefa jama’ar kasar da ta fi kowacce fitar da albarkatun mai a Afirka cikin halin kaka-ni-ka-yi.
A baya-bayan nan, mutane na farin cikin sayen man fetur mai sauki, wanda ake samu da rahusa sakamakon tallafin biliyoyin daloli da gwamnati ke baiwa masu shigo da man daga kasashen ketare.
Bayan kawo dalilai na kudi da dokoki, gwamnatin Nijeriya a yanzu ta kawo karshen tallafin man fetur.
A lokacin da masu sayen man fetur ke gwagwarmayar sabawa da sabon farashin sama da na baya, kasafin kudin da mutane ke kashe wa a gidajensu ke kare wa nan da nan.
Yadda farashin kayyaki ke ta tashi saboda kara farashin man fetur ya zama kalubale ga rayuwa musamman ga dalibai, gidajen da ba su da kudade da yawa ko masu kananan sana’o’i.
Kusan a kowacce rana Nijeriya na fitar da ganga miliyan biyu na danyen man fetur – a yankin Niger Delta. Amma kuma tun bayan a watan Yuni, ana sayar da litar man fetur kan Naira 550 a wasu biranen kasar, sama da farashin man watanni biyu baya.
Rashin samun damar zuwa makaranta
Ekanem, dalibi a Jami’ar Uyo jihar Akwa Ibom na daga cikin miliyoyin da ke jin radadin cire tallafin man fetur, inda har ta kai ga yanke ranakun da yake zuwa makaranta saboda tsadar kudin mota.
A kwanakin nan sau biyu kawai yake iya halartar azuzuwa. Ya shaida wa TRT Afrika cewa “Ba na jin kamar ni dalibi ne a yanzu haka, saboda daga cikin kwanaki biyar da ya kamata na halarci aji, sai sau biyu kawai na ke iya zuwa.
"Ba na iya zuwa aji, tare da fatan zan karbi rubutun wadanda suka halarta.”
Dalibi mai karantar likitanci Emmanuel Chibuike ya yi nuni da cewa ba wai batun kudin mota ne kawai lamarin ya shafa ba, “abinci da buga takardu sun yi tsada su ma sosai”.
Idayat Adebanjo, wadda ke da shagon gyaran gashi a Uyo, ba ta samun masu zuwa shagonta sosai kamar yadda yake a baya saboda mutane ba su da kudade a hannunsu, kuma ba sa son kashe kudi da yawa.
Ta ce “A baya ina karbar Naira 500 don yin kitso. Amma a yanzu na kara zuwa 800, yawan masu zuwa sun ragu.
"Gaskiyar zance, mutane na son biyan kudi kadan, kasa da yadda yake a baya, suna korafin kan kudin motar zuwa.”
Idayat da ke da yara maza uku, ta fara sana’ar kitso da gyaran gashi tun 2021, bayan ta biyo mijinta daga jihar Ogun da aka haife ta zuwa Uyo don ci rani.
Idayat Adebanjo ta yi korafi da cewa “Na saba ina baiwa yarana Naira 600 kowanne don zuwa da dawo wa makaranta kowacce rana, amma a yanzu ina biyan Naira 700 kawai ga su biyun.
"Babban dana na shirin fara jami’a wannan shekarar, kuma ba zan iya daukar nauyinsa ba saboda yadda aka kara kudin makaranta da yadda rayuwa ta kara tsada.”
Amfani a nan gaba
Tsawon shekaru tallafin man fetur ya janyo wa tattalin arzikin Nijeriya asara, inda mahukunta da masana tattalin arziki ke cewa ba talakawa ne ke amfana da tallafin da ake bayar wa ba.
Wasu ‘yan tsiraru ‘yan boko ne ke azurta kawunansu da wani bangare na kudadaden da ake ware wa tallafin man.
Alkaluma daga Hukumar kula da sha’anin man fetur ta Nijeriya na nuni da cewa amfani da man fetur a kasar a kowacce rana ya ragu zuwa lita miliyan 48.43 a watan Yuni, daga lita miliyan 66.9.
Hukumar ba ta bayar da dalilan da suka sanya aka samu raguwar adadin ba, amma wasu masu fashin baki na ganin hakan ba ya rasa nasaba da yadda mahukunta suka yi kokarin sanya idanu kan yawan man da ake shigo da shi da wanda ake sha kullum, wanda hakan ne ke fayyace yawan kudin tallafin man da ake bayarwa.
Abun da mafi yawan masana tattalin arziki suka tafi a kai shi ne “Ba za a iya ci gaba da biyan tallafin mai a Nijeriya ba.
"Shugaba Tinubu a watan da ya gabata ne ya sanar da janye tallafin man fetur, don kubutar da kasar daga durkushewa.”
A shekarar da ta gabata gwamnati ta kashe dala biliyan 10 saboda tallafin man fetur. Duk da ta kashe dala biliyan 2.41 a watanni biyar na farkon shekarar.
Nijeriya za ta iya samun rarar dala biliyan 5.10 a wannan shekarar saboda cire tallafin man da kuma sauye-sauye kan sha’anin sauyin kudi, inji Bankin Duniya a watan Yuni.
Gwamnatin ta bayyana za a yi amfani da kudaden da ake tara wa wajen gudanar da manyan ayyuka, kula da lafiya da ilimi, tare da magance talauci da rashin ayyukan yi, inda za a dinga dawo wa da talaka damar amfana da kudaden.
Shugaba Tinubu ya furta da kan sa kan irin wahalar da ‘yan Nijeriya ke sha saboda cire tallafin. Amma ya tabbatar da za a yi amfani wadannan kudade a nan gaba, a saboda haka jama’a su yi hakuri.
Kubutar da kudaden kasa
“Na yarda cewa wannan mataki zai kara wa jama’armu zafin nauye-nauyen da ke kansu. Ina jin radadin da kuke ji,” in ji Shugaban Kasa Tinubu a wani sakon talabijin da ya fitar na ranar Dimukradiyya ta Nijeriya.
Ya ce “Cire tallafin man fetur zai kubutar da albarkatu da kudadenmu da kowa ke bukata, wanda wasu ‘yan tsiraru suke kalmashe wa a baya.”
Wasu kwararru na cewa ya kamata gwamnati ta dauki matakan rage radadin da jama’a ke ji a wannan lokaci.
“A fadade ya kamata a bayyana irin yadda tashin farashin mai ya shafi rayuwar yau da kullum. Mai ne jinin gudanar da tattalin arziki a Nijeriya,” in ji Ubon Asa, masanin tattalin arziki da ke aiki a sashen nazarin tattalin arzikin ayyukan noma da ilmantar da manoma a Jami’ar Uyo.
Ya shaida wa TRT Afrika cewa “Mafi yawan kananan kasuwanci sun dogara ne kan amfani da injinan bayar da wuta kanana da ke amfani da fetur.
"Mai na kara tsada, kaya na kara kudi ta yadda mutane ba sa iya sayayya saboda nasu kudaden da suke samu ba su karu ba. Hakan ya sanya su rage sayen kayayyaki na jin dadi. Sai abun da yake dole na abinci, magani da makaranta.”
Farfado da matatun mai
Domin magance wadannan wahalhalu, Asa na da ra'ayin cewa dole ne gwamnati ta kara albashi tare da samar da tsarin sufuri mai sauki ga jama’arta.
Ya fada wa TRT Africa cewa “Za a iya dakatar da harajin da masu samar da kaya ke biya na wani dan lokaci, sannan a kara yawan wutar lantarkin da ake rarraba wa.”
Ya kuma yi kira da a yi sauye-sauye kan sha’anin kudi a bangaren has’anin mai da iskar gas a Nijeriya. “Bai kamata a yi kasuwancin mai a cikin Nijeriya da dalar Amurka ba, saboda hakan zai janyo tashin kudaden kasashen waje a kasuwannin canji, wanda hakan zai cutar da tattalin arzikin a cikin gida.”
Ya kuma bayar da shawarar inganta ayyukan tace mai a gida Nijeriya. “Abun da za a yi shi ne gwamnati ta farfado da matatun mai da muke da su yadda za su dawo aiki yadda ya kamata.
"Sauyin da muka gani a bangaren sadarwa na daidaita farashi, irin sa ya kamata mu gani a bangaren cire tallafin mai da gwamnati ta yi,” in ji Asa.