Sojoji sun rufe iyakokin Nijar bayan kifar da gwamnatin Bazoum Mohamed

Sojoji sun rufe iyakokin Nijar bayan kifar da gwamnatin Bazoum Mohamed

Sojoji a Jamhuriyar Nijar sun ce sun kifar da gwamnatin farar-hula ta Shugaba Mohamed Bazoum.
Sun ce an rufe dukkan iyakokin kasar har sai abin da hali ya yi./Hoto:TRT Afrika

Sojoji a Jamhuriyar Nijar sun ce sun kifar da gwamnatin farar-hula ta Shugaba Mohamed Bazoum.

Sojojin sun bayyana haka ne a wata sanarwa da suka karanta a gidan talabijin na kasar ranar Laraba da tsakar dare.

Sun ce an rufe dukkan iyakokin kasar har sai abin da hali ya yi, sannan suka kara da cewa an sanya dokar hana fita a kasar.

Mohamed Bazoum ya soma mulki ne a watan Afrilun 2021./Hoto:Reuters

“Mu, dakarun tsaro mun yanke shawarar kawo karshen gwamnatin Shugaba Bazoum,” in ji jagoran sojojin Laftanar Kanar Amadou Abdramane.

Yana bayanin ne kewaye da wasu sojoji tara. Ya kara da cewa “an soke dukkan hukumomi" na tsarin mulki a kasar.

Wannan lamari ya faru ne bayan sojoji da ke kula da fadar shugaban kasar sun toshe fadar shugaban kasar da gidansa da ke Yamai babban birnin kasar ranar Laraba da safe.

Wani sakon Twitter da aka wallafa a shafin fadar shugaban kasar daga bisani ya tabbatar da cewa wasu sojojin fadar sun tayar da yamutsi ranar Laraba.

Sai dai ya ce shugaban kasar da iyalansa suna cikin koshin lafiya.

Mohamed Bazoum ya soma mulki ne a watan Afrilun 2021 bayan ya lashe zaben shugaban kasar.

Juyin mulki sau hudu

Nijar ta yi fama da juye-juyen mulki sau hudu tun da ta samu 'yancin kai daga Faransa a 1960./ Hoto:Reuters

Jamhuriyar Nijar, wadda ta samu 'yancin kai daga Faransa a 1960, ta yi fama da juyin mulki sau hudu.

Na baya-bayan nan shi ne na watan Fabrairun 2010 wanda ya hambarar da gwamnatin Shugaba Mamadou Tandja.

Barazana ga dimokuradiyya

Jim kadan bayan mamaye fadar shugaban Nijar da sojoji suka yi, Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta bayyana damuwarta game da batun.

Shugaba Tinubu ya umarci Shugaba Talon ya tafi Nijar./Hoto:Fadar shugaban Nijeriya

Shugaban Nijeriya wanda shi ne shugaban ECOWAS, Bola Tinubu ya karbi bakuncin Shugaba Patrice Talon na Benin inda ya umarce shi ya tafi Nijar don tabbatar da zaman lafiya.

Kazalika kungiyar ta fitar da sanarwar da ke cewa "shugabancin ECOWAS ba zai lamunci duk wani tarnaki da zai shafi tafiyar da sha'anin mulki cikin doka ba a Nijar ko wani bangare na Afirka ta Yamma.

"Ya kamata masu hannu a wannan lamari a Jamhuriyar Nijar su fahimci cewa shugabancin ECOWAS da duk masu goyon bayan dimokuradiyya a fadin duniya ba za su lamunci duk abin da zai jawo rusa gwamnatin dimokuradiyya da aka kafa a kasar ba," a cewar sanarwar da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu.

Sauran shugabanni da hukumomi duniya sun yi tir da juyin mulki, ciki da har shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da na Kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat.

TRT Afrika