Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya MDD Antonio Guterres "ya yi kakkausar suka game da juyin mulki da aka yi" a Jamhuriyar Nijar.
Guterres ya nuna damuwarsa matuka kan tsare shugaban kasar Mohamed Bazoum da jami'an tsaron fadar shugaban suka yi, a cewar mai magana da yawunsa Stephane Dujarric a wata sanarwa da ya fitar, bayan juyin mulkin da aka yi a kasar ta Nijar.
"Sakatare Janar ya yi kira da a gaggauta kawo karshen duk wasu ayyukan da ka iya kawo cikas ga tsarin dimokuradiyya na Nijar," in ji Dujarric.
Shi ma Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi kira da a gaggauta sakin Shugaba Mohamed Bazoum.
Ranar Laraba wani gungun sojoji ya sanar da kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum a jawabin da suka yi a wani gidan talabijin na kasar.
Tuni dai kasashen duniya suka nuna damuwarsu tare da yin Allah wadai kan yunkurin ture gwamnatin farar-hula a kasar ta Jamhuriyar Nijar.
Kasashe da kungiyoyin da suka soki wannan juyin mulki sun hada da Kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS da Kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya da Faransa da Amurka.