An kama wasu mutane biyu da ake zargi da yunkurin cutar da shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema ta hanyar amfani da maita, in ji 'yan sandan ƙasar a ranar Juma'a.
Kakakin ‘yan sandan, Rae Hamoonga, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mutanen biyu, Jasten Mabulesse Candunde, mai shekara 42, da Leonard Phiri, mai shekara 43, ana zargin Nelson Banda, kanin dan majalisar da ke gudun hijira, Jay Banda, ya dauki hayar su don yi wa shugaban kasar sihiri.
Jay Banda ya tsere daga hannun ‘yan sanda ne a watan Agustan 2024 yayin da yake fuskantar tuhume-tuhume da laifin yin fashi da makami.
Ba a san inda yake ba. Mutanen biyun da ake zargin suna fuskantar tuhumar aikata laifin bokanci da kuma mallakar layu da zaluntar dabbobi.
“Wadanda ake zargin an same su da laya iri-iri, ciki har da hawainiya mai rai, kuma ana zarginsu da aikata aikata tsafi,” in ji Hamoonga, inda ya kara da cewa manufarsu ita ce su yi amfani da laya don cutar da shugaban kasa, Hakainde Hichilema.
Kakakin ‘yan sandan ya ce wadanda ake zargin sun bayyana cewa sun amince a biya su dala 7,400 don aikata sihirin.