Kasar Rasha da Nijar da ke karkashin mulkin sojoji tun bayan hambarar da gwamnati farar hula da aka yi a bara, sun amince da kara inganta hadin gwiwar soji, a cewar sanarwar da Ma'aiktar Tsaron Rasha ta fitar a ranar Talata.
A cewar kamfanin dillancin labaran Rasha, Mataimakin Ministan Tsaron Kasar Yunus-Bek Yevkurov da Alexander Fomin sun gana da Ministan Tsaron Nijar Salifu Modi wanda gwamnatin soji aka naɗa a kasar a ranar Talata.
"Wakilan sun bayyana mahimmancin inganta dangantakar Rasha da Nijar ta fannin tsaro, kuna sun amince su karfafa ayyukan hadin gwiwa don daidaita al'amura a yankin," in ji ma'aikatar, tare da kari kan cewa tana da kudurin ci gaba da tattaunawa kan "kara shirye-shiryen" Sojojin Nijar.
Ko da yake, ma'aikatar ba ta bayar da wani cikakken bayani game da shirye-shiryenta ba.
Majalisar mulkin sojin Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani ta karbi mulki bayan hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.
Janyewar Faransa
Gwamnatin Nijar ta fatattaki sojojin Faransa tare da datse duk wasu yarjejeniyoyin tsaro da kungiyar Tarayyar Turai, lamarin da ya sanya ƙawayenta na kasashen yammacin Turai fargabar cewa kasar za ta iya zama wata sabuwar kafa ga Rasha a yankin
Firaministan Nijar Mahamane Lamine Zeine wanda gwamnatin mulkin kasar ta nada Ali ya isa birnin Moscow a ranar Talata. A yayin zayarar, Zeine na shirin tattaunawa kan fadada hadin gwiwa da Rasha a fannonin tsaro da noma da kuma makamashi.
Ma'adinin Uranium da man fetur na Nijar da kuma muhimmiyar rawar da take takawa wajen yaki da masu kaifin kishin Islama a yankin Sahel na kara ba ta muhimmanci a fannin tattalin arziki da dabaru ga kasashen Amurka da Turai da China da kuma Rasha.