Wannan ne karo na biyu da Babban Bankin Ghana ke karin kudin ruwa a bana Photo/ Getty Images

Babban Bankin kasar Ghana ya kara kudin ruwa da maki 1.50 inda ya mayar da shi kashi 29.5 cikin 100.

Babban Bankin ya ce ya yi wannan karin ne daga kashi 28.0 domin dakile hauhawar farashi da kuma daidaita tattalin arzikin kasar.

Wannan karin dai na zuwa ne bayan Babban Bankin kasar ya yi tattaunawarsa ta biyu a bana domin yin bitar tattalin arzikin kasar.

Haka kuma wannan ne karo na biyu da bankin ke kara kudin ruwa a bana inda ko a watan Janairu sai da ya kara daga kashi 27.0 zuwa 28.0.

A bara kuwa sai da bankin ya kara kudin ruwa sau bakwai duk a yunkurin dakile hauhawar farashin kayayyaki da kuma daidaita tattalin arzikin kasar.

Jaridun Ghana sun ruwaito Dakta Ernest Addison wanda shi ne gwamnan bankin yana cewa, karin kudin ruwan ya zama tilas domin magance yadda ake samun karuwar hauhawar farashin kayayyaki.

Me masana ke cewa kan wannan karin?

Malam Shaibu Abubakar, mai sharhi kan tattalin arziki ne a kasar Ghana kuma ya shaida wa TRT Afrika cewa, Babban Bankin Ghana ya yi wannan karin ne domin rage yawan kudin da ke yawo a hannun jama’a.

“A ilimin tattalin arziki, idan hauhawar farashi ta yi yawa, hakan na nufin kudi da yawa na farautar kaya kadan da ke cikin kasuwa,” kamar yadda Malam Shaibu ya shaida wa TRT Afrika.

“Yaya za a yi a karbo kudin nan ko a rage kudin da ke hannun mutane? Wannan karin kudin ruwa hanya daya ce ta rage wadannan kudade,” in ji Malam Shaibu.

Ya bayyana cewa wannan karin yana tasiri matuka ga kudin ruwan da bankuna ke kara wa masu rancen kudi domin a cewarsa, idan kudin ruwa ya yi sama, gwiwar mutane kan yi sanyi wanda hakan zai sa za su rage zuwa banki domin karbar rancen kudi.

Sai dai ya bayyana cewa illar da wannan karin kudin ruwan zai yi zai sa jama’a su wahala kafin samun kudi, sa’annan a cewarsa zai shafi ‘yan kasuwa.

Malam Shaibu ya bayyana cewa yana sa ran nan gaba idan an samu saukin hauhawar farashin kayayyaki, jama’a za su samu sauki domin shi ma babban bankin zai iya rage kudin ruwan da yake karawa.

TRT Afrika da abokan hulda