An buɗe matatar man Dangote a 2023 a Legas inda ake sa ran cewa za ta taimaka wa matatun man ƙasar. / Hoto: Reuters

Ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin Dangote a ranar Lahadi ya bayyana cewa wasu manyan kamfanonin mai na hana matatar Dangote ɗanyen man fetur ta hanyar sayar da man fiye da farashin gwamnati ko kuma iƙirarin cewa babu ɗanyen man, wanda hakan yake tilasta wa kamfanin shigo da mai daga ƙasashen waje.

Matatar man wadda aka gina kan dala biliyan 20, wadda ya kamata ta zama mafi girma a Afirka da Turai, ta soma aiki a watan Janairu, sai dai tana ta gwagwarmayar neman man fetur domin tace gangar fetur 650,000 da ya kamata ta rinƙa yi a kullum.

Matatar na shigo da kusan sunduƙai 10 na fetur a duk wata, kamar yadda suka bayyana.

"Ko dai manyan kamfanonin mai da gangan suna neman ƙari ko kuma suna neman cewa babu ɗanyen mai a ƙasa," in ji Devakumar Edwin, wani babba a kamfanin mai na Dangote a wata sanarwa da ya fitar.

Ƙarin kuɗi

Ya bayyana cewa matatar man na biyan sama a dala miliyan shida fiye da farashin fetur ɗin a kasuwa, wanda hakan ya sa ta rage man da take tacewa da kuma dogara kan man da take shigowa da shi daga ƙasashe irin su Amurka. Wannan ne a cewarsa ya ƙara yawan kuɗin da ake kashewa.

Kamfanonin da ke haƙo da ɗanyen man fetur a Nijeriya ta ƙarƙashin ƙungiyarsu ta Oil Producers Trade Section (OPTS), ba ta mayar da martani nan take ba dangane da wannan zargin.

Ya kamata a ce matatar man ta Dangote tana samun gangar man fetur 325,000 a kullum daga kamfanoni na cikin gida kamar yadda tsarin da NUPRC a ƙasar da ke sa ido kan kamfanonin fetur ɗin ya samar.

Sai dai zuwa yanzu kamfanonin man sun gaza cika wannan aƙawari.

Wata dokar man fetur da aka yi a Nijeriya a 2021 ta samar da hukumomi biyu masu sa ido waɗanda suka haɗa da NURPC da NMDPRA.

Edwin ya kuma zargi NMDPRA da bayar da lasisin shigo da mai ga 'yan kasuwa da dama waɗanda ke shigar da gurɓataccen mai daga Rasha

Sai dai NMDPRA ita ma ba ta mayar da martani dangane da wannan zargin da ake yi mata ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ta bayyana.

Reuters