Majalisar Dinkin Duniya MDD ta kaddamar da wani bincike kan take hakkin dan'adam da kuma dokokin jinkai na duniya a yakin basasar da aka shafe watanni tara ana yi a Sudan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum akalla 12,000 tare da raba miliyoyi da matsugunansu.
"Kungiyoyin fararen-hula a Sudan da sauran masu shiga tsakani sun fara bayyana mana zarge-zargen cin zarafi masu tsanani da aka yi a Sudan," in ji Mohamed Chande Othman, shugaban tawagar binciken na majalisar.
"Wadannan zarge-zargen na nuna muhimmancin ajiya bayanai, da kuma wajibcin bincikenmu da bukatar kawo karshen rashin zaman lafiya nan-take," in ji Othman.
Othman ya kasance tsohon babban alkalin kasar Tanzaniya kuma daga cikin tawagarsa har da Joy Ezeilo, shugabar sashen shari'a a Jami'ar Nijeriya, da kuma Mona Rishmawi ta kasar Jordan da Switzerland, kana tsohuwar kwararriya mai zaman kanta wacce ta yi aiki da Majalisar Dinkin Duniya kan hakkin dan'adam a Somaliya.
'Hakkin dokar shari'a'
"Bangarorin biyu da ke yaki da juna suna da hakkin shari'ar duniya wajen kare duk wani farar-hula daga hare-hare da tabbatar da kai dauki da kuma kaurace wa kisan kai da tilasta gudun hijira da azabtarwa da tsare mutane ba bisa ka'ida ba, da kuma tilasta bacewar mutane ta ko wacce hanya," in ji Rishmawi.
''Za mu tabbatar an tantance duk wasu zarge-zarge da aka samu, sannan za mu gudanar da namu binciken ba tare da nuna son kai ba.''
Binciken zai mayar da hankali kan laifukan take hakkin dan'adam a rikicin da ke tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, da sauran bangarorin da ke fada da juna tun soma yakin ranar 15 ga Afrilu, 2023.
A cewar Joy Ezeilo, binciken zai fi ''mayar da hankali musamman ga cin zarafin mata da yara.''
Gayyatar ba da shaida
"Zarge-zargen fyade da ake yi wa galibi mata da 'yan mata da kuma zargin daukar yara kanana don amfani da su wajen yaki na daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a bincikenmu," in ji Ezeilo.
MDD ta bukaci dukkan bangarorin da ke rikici da juna su ba da hadin kai ga bincikenta tare da neman daidaikun mutane da al'umma da kuma kungiyoyi da su ba da shaida a asirce kan take hakkin dan'adam da ya gudana a Sudan a wannan lokaci da ake nazari a kai.
Tawagar masu binciken ta ce za a gabatar da bayanai ta baka kan sakamakon binciken farko da aka gudanar ga Majalisar Kare Hakkokin Dan'Adam a zamanta na hamsin da shida a watan Yuni zuwa Yulin 2024, sannan za a rubuta rahoto ga zauren MDD na hamsin da bakwai a watan Satumba zuwa Oktoba da kuma babban taronta na saba'in da tara a watan Oktoba ba 2024.
Fiye da mutane 13,000 aka kashe tun bayan soma yakin Sudan a watan Afrilu, a cewar wani kiyasi na kungiyar da ke tattara bayana kan tashe-tashen hankula, sannan Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane miliyan bakwai ne suka rasa matsugunansu.