Karar da Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ya sanya a karon farko a tarihi a hukumance ana tuhumar Isra'ila da aikata laifukan yaki. Hoto: AA

Bayan gwamnatin Afirka ta Kudu ta shigar da Isra'ila kara a Kotun Kasa da Kasa da ke Hukunta Manyan Laifuka (ICJ) bisa tuhumarta da aikata kisan kiyashi a Gaza, kusan lauyoyi 50 daga kasar suna shirya sabuwar kara ta daban don shigar da Amurka da Ingila kotu kan dalilan hada baki da Isra'ila da ke aikata laifukan yaki a Falasdinu.

Wannan kokari da Lauya Wikus Van Rensburg ke jagoranta, na da manufar gurfanar da wadanda suke hada baki a gaban kotun, kuma suna hada gwiwa da wasu lauyoyin Amurka da Ingila da tuni sun fara tattaunawa kan batun.

Rensburg na ta rubuta wasiku zuwa ga kasashe da dama da Kotun Kasa da Kasa a makonnin da suka gabata, yana neman da a gurfanar da Isra'ila da duk masu goya mata baya a gaban kotun, kuma sun fara shirin shigar da kasashen Yamma biyu kara.

"Dole ne Amurka ta dauki alhalin muggan laifukan da ta aikata," in ji Rensburg yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, inda ya yi karin haske kan yadda za a tuhumi Washington da Landan kan laifukan yakin da Tel Aviv ke aikatawa kan jama'ar Gaza.

Rensburg ya kuma bayyana yana samun goyon baya sosai. "Lauyoyi da dama sun yanke hukuncin hada hannu da mu a wannan kara. Da yawan wadanda suka nuna sha'awar Musulmai ne, amma ni ba Musulmi ba ne.

Sun ji cewa lallai dole ne ma su goya min baya, amma ni na yi amanna da abin da ake aikata wa ba daidai ba ne."

'Ya isa haka'

Abin da ya faru a Iraki misali ne, in ji shi, yana mai cewa babu wanda ya tuhume ta kan laifukan yakin da ta aikata a kasar ta Gabas ta Tsakiya, saboda ba a baiwa batun muhimmanci ba.

Amma yanzu mutane sun farga kan abin da ke afku wa a Falasdin ya kamaci a shigar da kara kotu, in ji lauyan na Afirka ta Kudu.

Ya kara da cewa "Amurka na ta bayar da kudade da kayan aiki don bai wa Isra'ila sararin aikata laifukan yaki."

"Babu wani d aya ce a dakata ya isa haka," in ji shi. Mummunan yakin da Isra'ila ke yi kan Gaza a yanzu ya shiga rana ta 101 - kuma ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa 23,968 tare da jikkata wasu 60,582, in ji jami'an lafiya, a yayin da Tel Aviv kuma ke nacewa kan ci gaba da kai hare-hare a dan karamin yankin na gabar teku.

Yiwuwar sanya takunkumi

Rensburg ya ce karar da Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila kotun ICJ za ta zamar musu jagora wajen shigar da Amurka da Ingila kara.

Idan aka kammala shari'ar karar da aka kai Isra'ila a ICJ tare da goyon bayan Afirka ta Kudu, Rensburg na yakinin za a iya saka wa Amurka takunkumai ko da kuwa ba ta yarda da hukuncin shari'ar ba.

Shari'ar ICJ din kuma za ta karfafa kasarar da za a kai gwamnatin Joe Biden, in ji shi.

Rensburg ya kuma ce shi da abokan aikinsa a Afirka ta Kudu na ci gaba da tuntubar lauyoyi a Amurka da Ingila a wani bangare na shirye-shiryen shigar da karar.

Hujjoji masu karfi

Da yake tunatar d acewar har yanzu Jamus na biyan diyyar muggan ayyukan da ta aikata a Namibiya, Rensburg ya ce "Dole a yanzu Amurka da dauki alhakin muggan laifukan da aikata. Dole ne ta karbi wannan abu da ta yi."

Ya yi nuni da an taba kai karar tsohon shugaban Amurka George Bush a shekarun 2000, lauyan na Afirka ta Kudu ya suna da yakinin za su samu nasarar wannan yunkuri nasu ta hanyar hada kai da aiki a matsayin kungiya daya.

Ya ci gaba da cewa Afirka ta kudu ta gabatar da manyan muhawarori da hujjoji masu karfi a gaban kotun ta Hague, kuma ana masa barazanar wai idan Afirka ta kudu ta samu nasara a kotun za a iya sake kai wa Isra'ila wani harin sabo.

A makon da ya gabata, wasu lauyoyi da a yanzu yawan su ya kai 47, sun rubuta budaddiyar wasika zuwa ga shugabannin gwamnatocin Amurka da Ingila, suna masu bayyana musu cewa ba su isa su tsallake hannu a wannan ta'annati ba.

TRT Afrika