A ranar Talata Sakataren harkokin gida na Kenya ya sha alwashin kawo ƙarshen fitintinu da wawason kaya da suka biyo bayan zanga-zangar adawa da gwamnati, "ta yin amfani da kowace irin hanya."
Kithure Kindiki ya faɗa a sanarwar da ya aike wa 'yan jarida cewa “dole a dakatar da taɓarɓarewar doka, tayar da fitina, da ɓarnata dukiyoyi.”
Aƙalla mutane 39 ne suka halaka a zanga-zangar, wadda ta fara ranar 18 ga Yuni kan ƙarin haraji, cewar rahoton Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Kenya KNCHR.
Hukumar da ke ƙarƙashin gwamnati amma tana da 'yancin saka-ido kan haƙƙoƙin ɗan'adam, ta ce yawancin mace-macen daga raunukan harbin bindiga ne kan masu zanga-zanga, sannan a wasu lokuta ma kan farar-hula.
'Karɓe' zanga-zanga
Kindiki ya ce, "Za a binciki iƙirarin faruwar ayyukan laifi da ake zargin jami'an tsaro, kuma za a ɗauki mataki".
Ya ce tashin hankalin, wanda ya faro sakamakon Ƙudurin Dokar Kuɗi ta 2024, gungun masu aikata laifi sun 'karɓe' zanga-zangar, waɗanda ke ci gaba da kawo tarnaƙi kan walwalar al'umma, da aikata ƙone-ƙone da tunzura al'umma.
Gwamnatin ta yaba wa jami'an tsaro saboda "nuna ƙwarewa da haƙuri" yayin da ta amsa cewa “an rasa rayuka, an ɓarnata dukiyoyi da suka kai na biliyoyin Shillings, kuma an yi yunƙurin ƙona gine-ginen Majalisar dokoki.”
“Yayin zanga-zangar yau wadda ta haifar da ɓarnata dukiyoyi da masu aikata laifi suka yi, jami'an tsaro a faɗin ƙasar sun tantance waɗanda ake zargi da shiga rigar masu zanga-zanga, kuma sun cafke su,” cewar Daraktan Binciken Laifuka cikin wata sanarwa.
Neman murabus ɗin shugaban ƙasa
Sanarwar ta ƙara da cewa, “A Nairobi da kewayenta, an kama mutum 204 da mutum 35 a yankunan gaɓar teku, da mutum 18 a Nyanza da 11 da 4 a Kwazazzabon Rift da yakunan gabashi.”
An samu ƙaruwar jami'an tsaro bayan ɓarkewar zanga-zangar a Kenya wadda Dokar Kuɗi ta 2024 ta haddasa.
Shugaba William Ruto ya ba da kai ranar Larabar da ta gabata, kuma ya sanar da cewa ba zai sanya hannu kan ƙudurin dokar ba. Amma kuma, zanga-zangar ta koma ta yin adawa da gwamnati, inda mutane ke kiran shugaban ƙasar ya sauka.
Motocin sojoji da motoci masu sulke na ɗaukar jami'ai, sun yi ta sintiri a Nairobi, tare da sojoji ɗauke da muggan makamai, waɗanda ke dafa wa 'yan sanda don kawar da ruɗani, da sace-sace da ɓarnata dukiya.