Rikicin Boko Haram a Nijeriya ya yi sanadin raba miliyoyin mutane da muhallansu. / Hoto: AA

Kotun Tarayyar Nijeriya ta kama mayaƙan Boko Haram da masu ɗaukar nauyinsu 125 da laifuka iri daban-daban waɗanda ke da alaƙa da ta’addanci a wasu jerin shari’o’i da aka gudanar a wannan makon, kamar yadda ofishin Atoni Janar na Nijeriya ya tabbatar.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu tun daga shekarar 2009, lamarin da ya haifar da matsalar jin kai a yankin arewa maso gabashin Nijeriya tare da matsa wa gwamnati lamba domin kawo karshen rikicin.

Kamarudeen Ogundele, wanda shi ne mai magana da yawun ofishin Atoni Janar na Nijeriya a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ya bayyana cewa “an kama su da laifukan ta’addanci da ɗaukar nauyin ta’addanci, bayar da tallafin kayan aiki, da kuma shari'o'in da suka shafi Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta kasa da kasa (ICC)."

Lokaci na ƙarshe da aka gudanar da irin waɗannan shari’o’i na wadanda ake zargi da ta’addancin Boko Haram an yi su ne a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2018, inda aka kama mutum 163 da laifi, aka kuma saki 887.

Ogundele ya kara da cewa daga cikin waɗanda aka kama da laifi a shari’ar baya da aka gudanar, mutum 400 waɗanda suka kammala zamansu na gidan yari an kai su cibiyar kula da lafiyar ƙwaƙwalwa ta Operation Safe Corridor a Gombe da ke arewa maso gabashin Nijeriya domin sauya musu tunani da cire musu tsatsauran ra’ayi a zukatansu da kuma sake mayar da su a cikin al’umma”.

Kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da 'yan mata sama da 270 a wata makaranta a garin Chibok da ke arewa maso gabashin kasar a cikin watan Afrilun 2014, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce kuma ya haifar da fafutikar " # Bring Back Our Girls " a duniya, duk da cewa fiye da rabin 'yan matan sun dawo, da yawa a matsayin uwayen yara da yawa.

TRT Afrika