Kamfanin Man Fetur na Nijeriya NNPCL ya ce za a fara sayar da man Matatar Dangote a kasuwannin ƙasar ranar 15 ga watan Satumban 2024.
NNPCL wanda ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis ya ce kasuwa ce za ta yi halinta wajen tantance farashin kayayyakin.
Wannan ci gaban ya biyo bayan fara tace man fetur da matatar Dangote ta fara aikinsa a farkon makon nan. NNPCL ya ce a yanzu kamfanin da gwamnati sun cire hannayensu kacokan a kan sanya farashin fetur a kasar.
Akan batun fara daukar mai daga Matatar Dangote, wani babban jami’in NNPC Adedapo Segun ya ce kamfanin na NNPC yana jiran wa’adin ranar 15 ga Satumba da matatar ta samar.
Segun ya ce babu wani mai tunani da zai ji dadin karancin man fetur da ake fama da shi a halin yanzu, ya kara da cewa NNPCL na da gidajen mai kusan dubu a duk fadin kasar, kuma yana hada kai da ‘yan kasuwa don “tabbatar da cewa tasoshin sun bude da wuri kuma ba su rufe da wuri ba, don samar da isasshen mai da zai wadata don biyan bukatun ‘yan Nijeriya.”
Ya kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa: “Muna kuma jan hankalin hukumomin da abin ya shafa don ganin an hana karkatar da man da kuma tabbatar da isar da shi a kan lokaci zuwa dukkan tasoshin.
Ya kamata a sassauta ƙarancin nan da ƴan kwanaki masu zuwa yayin da ƙarin tasoshi suka sake daidaitawa tare da fara aiki.”
Kalaman Segun na zuwa ne bayan da Gwamnatin Tarayya ya ayyana cewa za a yi gagarumin aikin samar da mai a karshen makon nan.
NNPCL ya bai wa Dangote gangar ɗanyen mai miliyan 30
Kamfanin NNPC ya kuma ce ya zuwa yanzu ya samar da gangar danyen mai miliyan 30 ga matatar ta Dangote, inda ya tsara ba da ƙarin ganga miliyan 17 nan ba da dadewa ba.
Kamfanin ya ce zai samar da ganga miliyan 6.3 a watan Satumba da kuma ganga miliyan 11.3 a watan Oktoba. “Mun kawo wa Dangote kusan ganga miliyan 30, miliyan 6.3 a wannan watan, kuma za mu samar da miliyan 11.3 a watan Oktoba,” in ji shi.
An yi nuni da cewa, ganga miliyan 6.3 za a kai su ne a cikin kaya guda bakwai amma ta nuna damuwa cewa farashin man fetur a halin yanzu bai nuna gaskiyar kasuwa ba.