Za a sayar da duk buhu daya mai nauyin kilo 50 a kan N40,000 maimakon farashinta na kasuwa na N90,000.

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce ma’aikatan gwamnati da ke da katin shaidar 'yan ƙasa na (NIN) ne kadai za a ba su izinin sayen shinkafar da aka rage wa farashi duk buhu ɗaya mai nauyin kilo 50 a kan naira 40,000.

A ranar Juma'a ne gwamnatin tarayyar ta ƙaddamar da shirin shiga tsakani a hukumance na sayar da tallafin shinkafa domin magance matsalar abinci da ake fama da ita a kasar.

Shirin, wanda Ministan Noma da Samar da Abinci Sanata Abubakar Kyari ya ƙaddamar na da nufin samar da shinkafa da sauki ga ‘yan Nijeriya musamman marasa galihu da masu ƙaramin ƙarfi.

A yayin da yake ƙaddamatr da shirin, Minista Kyari ya ce an ɗauki matakin sayar wa ma'aikata masu katin shaidar zama 'yan ƙsa ne kawai don a daƙile badaƙal da cuwa-cuwa a harkar.

Gidan Rediyon Tarayya na ƙasar FRCN, ya rawaito cewa, sakamakon tsadar kayan abinci da kuma wahalhalun da ‘yan kasa ke fama da su, gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar noma da samar da abinci ta fara sayar da shinkafa a kan farashi mai rangwame na Naira 40,000 kan kowane buhu mai nauyin kilogiram 50, idan aka kwatanta da yadda ake sayar da shinkafar a farashin kasuwa kan naira 90,000.

A cewar ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, tallafin abincin ya zo kan lokaci domin wannan na daya daga cikin yunƙurin da gwamnati mai ci ke yi na ganin an shawo kan matsalar tsadar abinci ta hanyar sakin metric ton 42,000 na kayayyakin Abinci iri-iri da kuma metric ton 30,000 na shinkafa ga marasa galihu a Nijeriya.

Sanata Kyari ya ce Gwamnatin Tarayya ta san irin kalubalen da ke iya tasowa, ta tura na’urorin gwamnati da dama, tare da sanya wasu tsare-tsare da sharuddan tabbatar da gaskiya da isarwa da kuma samun nasarar wannan aiki.

Sanata Sabi ya jaddada cewa shirin zai taimaka matuka wajen magance matsalar tattalin arziki da wasu ‘yan Nijeriya ke fuskanta.

Za a iya samun shinkafar a cibiyoyin da aka ware a fadin kasar nan, kuma gwamnatin tarayya ta ba da tabbacin cewa za ta sanya ido kan shirin domin tabbatar da gaskiya da kuma samun nasara.

TRT Afrika