Babban Bankin Nijeriya CBN ya sanar da cewa zai sayar wa ‘yan canji dala kan naira 1,580.
Bankin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarancin dalar a kasuwannin bayan fage.
Bankin ya sanar da cewa zai sayar da dalar Amurka 20,000 ga kowane ɗan canji mai rajista a kan naira 1,580 domin cike giɓin da ake da shi.
Sai dai bankin ya ce bai amince ga ‘yan canjin su sayar da dalar sama da kashi ɗaya cikin 100 na kan yadda suka same ta daga CBN ba.
CBN ɗin ya buƙaci ‘yan canjin da suke da rajista kuma suka cancanta da ke buƙatar waɗannan kuɗaɗe kan su biya kuɗinsu a naira ga asusun saka kuɗi na babban bankin.
Hakazalika bankin ya ce hada-hadar biyan kuɗin da bayar da shaida da karɓa dala 20,000 ɗin duka ‘yan canjin za su iya zuwa ofisoshin babban bankin da ke Abuja ko Awka ko Kano ko kuma Legas.
Wannan matakin da CBN ɗin ya ɗauka shi ne na baya-bayan nan da bankin ya ɗauka domin daidaita farashin dala da naira a kasuwar canji.
Haka kuma matakin na zuwa ne a daidai lokacin da aka rinƙa sayar da dalar a kan naira 1,670 a kasuwannin bayan fage a faɗin ƙasar.
A baya CBN ɗin ya ta ɗaukar jerin matakai domin tabbatar da cewa naira ta samu tagomashi a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje, sai dai lamarin ya ci tura, inda dalar ke ci gaba da tashi.