Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja babban birnin Nijeriya ta bayar da umarnin dakatar da asusun ajiya 1,146 mallakar wasu mutane da kamfanoni waɗanda ake zargi da saɓa dokoki daga ciki har da halasta kuɗin haram da hannu a illata darajar naira.
Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin dakatar da asusun ajiyar har sai an kammala bincike, kamar yadda wata sanarwa da Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Nijeriya Zagon Ƙasa EFCC da ta fitar ta bayyana.
Alƙalin ya ce, “binciken wucin-gadi da aka gudanar ya nuna cewa asusun ajiyar na da alaƙa da mutanen da ke amfani da manhajojin kirifto domin yi wa naira zagon ƙasa da kuma halasta kuɗin haram,” in ji sanarwar ta EFCC.
Alƙalin ya bayyana cewa akwai buƙatar a ci gaba da ajiye kuɗaɗen a banki har sai an kammala bincike ko kuma an yanke hukunci.
Hukumar ta EFCC ta bayyana cewa asusun da aka dakatar sun shafi kamfanonin ayyukan gona da sufuri da ƙananan bankuna da sauransu, kamar yadda hukumar ta bayyana.