Kotun Hukunta Manyan Laifuka da ke birnin Hague ranar Alhamis ta soma sauraren karar da Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila a gabanta bisa zargin kisan kare-dangi a Gaza.
Afirka ta Kudu ta shaida wa Kotun Hukunka Manyan laifuka cewa Isra’ila tana aikata kisan kare-dangi a Gaza lamarin da ya jefa daukacin yankin cikin bala'i.
Lauyoyin kasar sun ce yaki na baya-bayan nan da Isra'ila ta kaddamar a Gaza yana cikin zaluncin da ta yi gomman shekaru tana yi wa Falasdinawa.
Zaluncin Isra’ila a Gaza ya kusa sa mutanen Zirin Gaza "su fada bala’in yunwa ", kamar yadda wani babban lauyan Afirka ta Kudu ya shaida wa babbar kotun ta Majalisar Dinkin Duniya ranar Alhamis.
Isra'ila ta musanta cewa tana yi wa Falasdinawa kisan kare-dangi duk da yake kawo yanzu ta kashe fiye da mutum 23,000, galibinsu mata da kananan yara, sannan ta jikkata kusan mutum 60,000, haka kuma ta raba kashi 85 cikin dari na mutum miliyan 2.3 da ke Gaza da muhallansu. Kazalika ta rusa fiye da kashi 60 na gine-ginen yankin.

Shari'ar da aka soma ranar Alhamis, wadda ka iya kwashe shekara da shekaru ana yinta, za ta kuma mayar da hankali kan halascin kasar Isra'ila wadda Yahudawa suka kirkira bayan kisan kiyashi da 'yan Nazi suka yi musu.
Kazalika za ta fito da matsayin Afirka ta Kudu: jam'iyyar da African National Congress da ke mulkin kasar ta dade tana kwantanta gallazawar da Isra'ila ke yi wa al'ummar Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan da irin tarihin kasar wadda Turawa tsiraru suka yi wa mulkin mulaka'u da ya hana bakaken-fata sakat har sai a shekarar 1994 da suka samu 'yanci.
A lokuta da dama Isra'ila tana kallon Majalisar Dinkin Duniya da kotunan duniya a matsayin wadanda ba su da adalci. Amma yanzu ta ce za ta tura manyan lauyoyi zuwa Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta [ICJ] domin su kare ta daga zargin yin kisan kare-dangi a yankin Gaza da aka mamaye.