Za a iya kwashe mako biyar ba a kammala gyara wayoyin da suka lalace na cikin ruwa ba waɗanda suka sa ake samun katsewar intanet a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka, a cewar hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa ta Ghana ranar Asabar.
Lalacewar wayoyin ta sa an samu gagarumar katsewar intanet lamarin da ya shafi harkokin kasuwanci, da suka haɗa da bankuna da kamfanonin sadarwa da na hada-hadar kuɗi da ma kasuwannin hannayen-jari.
Hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa na Ghana ta ce ta gana da kamfanoni huɗu da ke aikin gyara wayoyin da ke ƙarƙashin ruwa - Africa Coast to Europe (ACE), MainOne, mallakin Equinix, South Atlantic 3 (SAT-3) da kuma the West Africa Cable System (WACS) - da kuma kamfanonin sadarwa.
Ta ce kamfanonin sun gaya mata ainihin wurin da wayoyin suka lalace kuma sun shirya tura ma'aikata domin gudanar da gyaran.
"Kamfanonin da ke gyaran wayoyin sun shaida mana cewa za su kwashe aƙalla mako biyar suna aiki kafin komai ya koma yadda yake," in ji hukumar.
Ranar Juma'a kamfanin MainOne ya ce ƙwarya-ƙwaryar binciken da suka yi ya nuna cewa wayoyin sun katse ne sakamakon wani motsi da ƙasa ta yi a cikin ruwa lamarin da ya shafe su.