Daga Maxwell Agbagba
TRT Afrika, Accra
Ƙarfe 7.18 na safiya, a ranar Lahadi mai cike da walwala a wajen da yawan mutanen ƙasar Ghana a Accra, yayin da suke shirin tafiya coci ko wasu harkokinsu, ba tare da hayaniyar ranakun mako da aka saba ba.
Kwatsam, sai jerin wasu girgiza suka katse musu walwalarsu. Kururuwar "girgizar ƙasa... girgizar ƙasa" ta cika kaure, sai kuma mutane suka shiga rige-rige cikin ɗimuwa, don neman wurin da za su tsira.
Za ka ɗauka mutanen unguwannin da ke zaune a inda za a iya samun girgizar ƙasa, za su saba da rayuwa tare da motsin ƙasa.
Amma kamar yadda Nancy Monye ƴar shekara 18 ta tabbatar, babu adadin wayar da kai da zai kwantar da hankalinka a kan girgizar ƙasar da za ta iya faruwa a kowane lokaci.
Iyalin Nancy na zaune ne a wata unguwa da ke bayan gari da ake kira Kasoa a babban birnin na Ghana. Kamar galibin mazauna birni, yawan faruwar abubuwa masu nasaba da girgizar ƙasa a ciki da kuma kewayen Accra a wannan shekarar yana damun ta.
"Ina ji a jikina babbar girgiza na nan tafe. Nan ne nake zama tare da iyayena; ba zan iya komawa wani wajen ba," ta gaya wa TRT Afrika.
Motsin ƙasa na farko ya girgiza Accra da safiyar ranar 12 ga watan Nuwamba. Yana da ƙarfin 3.8 a ma'aunin Richter, kuma ya biyo bayan wani motsin ƙasa mai girman 2.8 da ya faru ranar 10 ga watan Maris.
A ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2022 wasu sassan babban birnin sun fuskanci motsawar ƙasa sau uku a cikin sa'o'i biyar. Na farkon ya faru ne da misalin ƙarfe 6 da minti 53 na safe a yammacin Accra, sai kuma faruwar na biyu da ƙarfe 10 na safe a wannan wajen dai. Na ukun ya faru ne da misalin karfe 11 da minti 53 na safe.
A kan gaɓa
Wasu ƙasashen Afrika sun fuskanci manyan girgizar ƙasa a cikin gomman shekaru da suka wuce, inda ta baya bayan nan ita ce wacce ta faɗa wa Morocco a watan Satumba.
Ankararwa daga hukumar kula da yanayin ƙasa ta Ghana (GGCA) game da faruwar abubuwa masu nasaba da girgizar ƙasa a yankin da ke nuna yiwuwar faruwar girgizar ƙasa mai ƙarfi, ya ƙara kiɗima mutane.
Johnson Quaye, ɗan shekara 25 da haihuwa, mazaunin Weija Kasoa Ridge, ya sadaƙar yana zama a yankin da yake da alamun girgizar ƙasa. Abin da ya fi damun shi, shi ne yadda mazauna wurin dayawa ke sare itatuwa suna gine-gine.
"Cikin irin hanzarin da gine-ginen kankaren ke tashi abin damuwa ne," in ji Johnson.
Gargaɗi daga mahukunta a galibin lokaci ba a sauraron shi. Johnson ya san cewa wataƙila yankin ya girbi abin da ya shuka, amma ya amince da cewa ba wani abin ku zo mu gani shi ko wani za su iya yi a kan hakan ba.
Rashin nuna damuwa shi ne kariyarsa a yanzu. "Wato kamar jiran bala'i ya faru ne. Ba ni da zaɓi face na ci gaba da zama a nan," ya ce.
Ƙarancin mayar da martani
Nicholas Opoku, babban jami'i mai kula da lamuran girgizar ƙasa na hukumar GGSA, ya ce bai damu da afkuwar girgizar ƙasa mai ƙarfi ba kamar yadda ya damu da shirya mata da Accra ke yi.
"Idan waje na fuskantar motsawar ƙasa akai akai, hakan na nufin babba sosai na daf da faruwa. Mun fuskanci manyan girgizar ƙasa a jere a baya," ya faɗa wa TRT Afrika.
"A halin yanzu, ba mu shirya wa hakan ba. Dole ka shirya wa girgizar ƙasar da aka yi hasashen faruwarta a kimiyyance sosai. Ɗaya daga cikin muhimman abubuwa shi ne samar da yanayin mayar da martani yadda ya kamata. Rage tasirin ta fuskar samar da yanayin mayar da martani zai ɗauki lokaci mai tsawo."
Opuku ya tuna yadda wani rahoto da aka haɗa bayan afkuwar mummunar girgizar ƙasa a shekarar 1939 ya bayar da shawarar ɗaukar wasu matakai, bisa lura da tasirin motsawar ƙasa.
"Rahoton ya bayar da shawarar cewa a tayar da babban birnin zuwa wani yankin da fi zama tsakiyar Ghana," ya ce.
Girgizar ƙasar shekarar 1939,mai girman 6.6,ita ce mafi muni a tarihin ƙasar ta Afrika ta Yamma, ta ritsa da mutane 17 sannan ta raunata ƙarin wasu 133.
Hukumar Bayar Da Agajin Gaggawa ta Ghana ta soki yin gine gine barkatai a wuraren da aka gano suna da matsala shi ke ƙara wa Accra yiwuwar fuskantar girgizar ƙasa.
Seji Saji Amedonu,babban daraktan hukumar mai kula da ƙwarewa, ya yi imani cewa wajibi ne hukumomi su sa ƙafar wando ɗaya da yin gine gine barkatai ba bisa ƙa'ida ba a yankin Weija ba tare da ɓata lokaci ba.
A nata ɓangaren, hukumar GGSA tana ta gudanar da tarurrukan wayar da kan jama'a a makarantu da kasuwanni da sauran wurare domin ilmantar da jama'a game da abin da za su yi lokacin girgizar ƙasa.
Yayin da Ghana ke fama yiwuwar fuskantar girgizar ƙasa, buƙatar yin shiri ta ɗara ta kowanne lokaci a baya.
Kururuwa cike da firgici ta girgizar ƙasar da ta gabata, na tuna wa kasar ta kare tushenta daga tasirin girgizar ƙasa.