Dubban 'yan gudun hijira ne suke ci gaba da kwarara zuwa Burundi daga gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo tun bayan da 'yan tawayen ƙungiyar M23 suka ƙwace birnin Bukavu, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gida ta Burundi ta sanar a ranar Lahadi.
‘Yan tawayen sun ƙwace birnin ne a ranar Juma’a a wani mummunan farmaki da suka kai yankin lamarin da raba dubban mutane da matsugunansu.
Ministan harkokin cikin gida na Burundi Martin Niteretse ya tabbatar da cewa 'yan gudun hijirar na ci gaba da tsallakawa zuwa Burundi, kana gwamnati na kan tantance adadinsu.
"Dubban 'yan gudun hijira daga Kongo suna tserewa ne saboda tsoro da fargabar cewa an ƙwace birnin Bukavu," kamar yadda ministan ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP.
Dubbai sun tsallaka iyaka
'Yan gudun hijirar sun tsere ne daga yankin Kamanyola na DRC inda suka ratsa ta Kogin Ruzizi kana suka nemi mafaka a lardin Cibitoke da ke arewa maso yammacin ƙasar Burundi, a cewar wata ƙungiya mai zaman kanta daga ɓangaren iyakar Burundi.
“Fiye da mutane 10,000 ne daga cikin 'yan gudun hijirar, wasu kuma suna kan hanyar isowa,” in ji majiyar wadda ta buƙaci kada a bayyana sunanta.
A ranar Juma'ar da ta wuce ne, jami'ai suka ce Burundi ta rufe wata babbar hanya ta kan iyaka da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a wani mataki na rage kwararar 'yan gudun hijira.
Tun dai daga watan Oktoban shekarar 2023, sojojin Burundi suka tura dakaru fiye da 10,000 zuwa gabashin Jamhuriyar Dimokuaɗiyyar Kongo, domin tallafa wa sojojin ƙasar wajen yakar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.