Rikici tsakanin Ethiopia da Somalia, da jigilar makamai suka ƙara ta'azzara shi, na barazana ga ƙwarya-ƙwaryar zaman lafiyar da ake da shi a yankin Kusurwar Afirka wanda hakan ke bayar da dama ga ƙungiyar tayar daƙayar baya ta Al Shabab, in ji ƙwararru.
Tun watan Janairu yankin ya shiga halin ɗarɗar a lokacin da Ethiopia ta sanar da cewar za ta yi amfani da gaɓar tekun Somaliland, yankin da ya ɓalle daga Somalia.
Somalia ta mayar da martani da kusantar Masar wadda ita ce babbar abokiyar hamayyar Ethiopia a yankin.
Masar na da tata matsalar da Ethiopia, musamman game da madatsar ruwa ta Grand Renaissance da take ginawa a Kogin Nilu wanda Alkahira ke wa kallon barazana ga inda take samun ruwan sha.
A ranar 14 ga watan Agusta, Shugaban Ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mohamoud ya sanar da ƙulla babbar yarjejeniyar ayyukan soji da Masar.
Tuni aka kai makamai har sau biyu zuwa Somalia -a makon da ya gabata ne jirgi na biyu ya isa ƙasar.
Masu nazari na cewar wannan lamari na kawo damuwa.
"Somalia na shigar da ƙarin makamai cikin ƙasar a yayin a rikicin ke ta'azzara. Duba ga rashin gaskiya da raunin kula da makaman, wannan abu ne mai sanya damuwa," in ji Omar Mahmood, na Ƙungiyar Sanya Idanu Kan Rikice-Rikicen Ƙasa da Ƙasa (ICG).
Ma'aikatar Harkokin Wajen Ethiopia ta bayyana damuwarta musamman game da yiwuwar mayaƙan Al Shabab ta samun makaman.
'Taɓarɓarewar dangantaka'
Somalia ta kuma ƙara yin barazanar korar sojojin Ethiopia da aka kai ƙasar don yaƙi da Al Shabab tun 2007.
A ƙarshen shekarar nan wa'adin zaman sojojin zai ƙare, kuma a karon farko Masar ta bayyana cewa za ta maye gurbin Ethiopia a ayyukan sojin.
Haka kuma Somalia na iya tursasa wa Ethiopia ta kwashe sojojinta 10,000 da ta jibge a kan iyakarsu don hana shigar 'yan tayar da ƙayar baya ƙasar.
Samira Gaid, wata mai nazari kan tsaro da ke Mogadishu, ta ce Somalia tana yin wannan barazana ce da zummar tanƙwara Ethiopia don kada ta zama ƙasa ta farko da za ta amince da 'yancin kan Somaliland.
Amma yiwuwar rasa ƙwararrun sojojin Ethiopia ta sanya fargaba a kudu maso-yammacin Somalia yankin da ta'addancin Al Shabab ya fi shafa.
"Idan Ethiopia da Somalia ba su haɗa kai ba, idan aka samu ƙarin taɓarɓarewa a alaƙarsu ta tsaro, al Shabab ce za ta yi nasara... za su iya amfani da giɓin da aka samu don cim ma manufarsu," in ji Mahmood.
Yunƙurin ƙasashen waje na kwantar da tarzomar bai yi wani babban tasiri ba.
Turkiyya ta karɓi baƙuncin taro har sau biyu tsakanin Ethiopia da Somalia, a watannin Yuli da Agusta.
Ba a iya gudanar da zama na uku ba a Ankara a makon da ya gabata.
"Yana da wahala a samu wani cigaba saboda wannan lamari da yake ƙara ta'azzara," in ji Gaid.
Masu nazari na cewa, babu alamun za a gwabza babban yaƙi, amma ana ci gaba da zargin juna.
A ƙarshen makon jiya, Somalia ta zargi Ethiopia ta kai makamai zuwa yankin arewa maso-gabashin Puntland, wani yanki da shi ma ya ɓalle, kuma ya ayyana cin gashin kai a 1998.
"Waɗannan ayyuka sun ci karo da ƙarfin ikon mulkin Somalia, kuma suna da tasiri babba ga tsaron ƙasa da yanki," in ji wani saƙo da ma'aikatar harkokin wajen Somalia ta fitar ta shafin X.