Kyaftin Ibrahim Traore ya kwace mulki ta hanyar karfin soji a watan Oktoban 2022. Photo: Rueters

Shugaban mulkin soji na Burkina Faso, a wata tattaunawa da ya yi, ya tabo batun takun sakarsu da Faransa, inda ya ce kasarsa ‘ba makiyar jama’ar Faransa ba ce’ amma suna adawa da ‘manufofin’ gwamnatin Faransa.

Bayan da Traore ya hau mulki a watan Satumban 2022 ne Faransa ta kwashe sojojinta daga kasar da ta yi wa mulkin mallaka sakamakon tsamin da alakarsu ta yi.

“Mu ba makiyan jama’ar Faransa ba ne, manufofin masu mulkar Faransa ne suke zama matsala a Afirka,” in ji Traore a yayin wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin ta kasar a yammacin Larabar nan.

Ya ce “Matukar wata kasa ba ta da niyyar mulkin danniya… to babu matsala,”

Hadin kai da yin kwaskwarima

“Dole mu yarda mu kalli juna a matsayin abu daya mai matsayi da kima daya… kuma mu yarda cewa akwai bukatar yin garanbawul ga hadin kanmu.”

Traore ya tabo batutuwan dangantakar Burkina Faso da Faransa tun tale-tale.

Ya ce “Sun kawo mutane sun sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama… wadanda suka hana mu samun ci gaba.”

“Ba iya Faransa ce kadai ke da halin mulkin danniya ba, akwai wasu kasashen ma daban.”

Sabbin kawaye

Traore ya kuma bayyana cewa Faransa ta gaza taimaka wa sojojin Burkina Faso a yayin da take yaki da ‘yan ta’adda.

“Muna da sabbin kawaye da suke taimaka mana da kayan aiki da wasu hanyoyi,” in ji shi, amma bai bayyana ko su waye ba.

Tun bayan ficewar Faransa a watan Janairu, Burkina Faso ta karfafa alakarta da Rasha, kawa ga sojojin da ke mulki a Mali mai makwabtaka da ita.

A watan Yuli Traore ya gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a yayin Babban Taron Rasha da Afirka a Birnin Saint Petesburg, kuma a makon da ya gabata ya gana da wakilan Rasha kan karfafa hadin kai a ayyukan soji.

Hadin kai da Iran

A ranar Litinin din da ta gabata, Ministar Harkokin Wajen Burkina Faso Olivia Rouamba, ta tattauna da Shugaban Iran Ibrahim Reisi a Tehran, inda ta bayyana fatan karfafa hadin kai da kasar.

Kasar wadda ke fama da talauci kuma ba ta da iyaka da teku, na fama da hare-haren ‘yan ta’adda da ke da cibiya a Mali tun 2015.

Wata kungiya mai sanya idanu ta bayyana cewa an kashe sama da fararen hula da sojoji 16,000 a Burkina Faso sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda.

An kuma raba sama da mutum miliyan biyu da matsugunansu, inda aka samu rikicin dan adam mafi muni a Afirka.

A watan Janairun 2022 ne sojoji suka kifar da Shugaba Roch Marc Christia Kabore daga kan mulki.

A watan Satumba kuma Traore mai shekaru 34 ya kifar da Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba.

TRT Afrika