Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi karin haske kan batun dakatarwar da gwamnatinsa ta yi wa tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele.
Shugaba Tinubun ya yi karin bayanin ne a yayin da yake tattaunawa da ‘yan Nijeriya mazauna Faransa a wata ziyarar aiki da ya kai kasar.
Shugaba Tinubu ya ce harkar hada-hadar kudi a karkashin Emefiele ta lalace a Nijeriya. Ya bayyana cewa wadanda ke zaune a wajen kasar ba su iya tura kudi ga iyayensu da ‘yan uwansu sakamakon farashin canji iri daban-daban.
“Bangaren hada-hadar kudi ya lalace. Mutane kadan sun kudance amma kuma ku da kanku kun daina tura kudi gida ga iyayenmu da ke cikin talauci. Farashi daban-daban, amma duk ta kare a yanzu.
“Mutumin yana hannun hukumomi. Ana yin wani abu a kan hakan. Za su warware tsakaninsu,” in ji shi.
“Muna da matsalolin tsaro a kasa. Watakila ta haka suke kara rura wutar rashin tsaro; dole mu dubi komai. Za mu sauya tsarin hada-hadar kudi; zai yi muku aiki,” kamar yadda Shugaba Tinubu ya bayyana.
A ranar 9 ga watan Yuni Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin dakatar da Godwin Emefiele tare da bayar da umarnin gudanar da bincike kan wasu zarge-zargen da ake yi masa.
Bayan an dakatar da shi sai hukumar DSS ta kama shi a Legas inda aka kai shi Abuja domin ci gaba da bincike.
Tuni Folashodun Adebisi Shonubi ya karbi jagorancin babban bankin a matsayin gwamnan bankin na riko.