Mali, Senegal, Somalia da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun yi Allah wadai da mummunan harin ta'addanci da aka kai a ranar Laraba a masana'antar kayan tsaro ta Turkiyya a babban birnin ƙasar.
"Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na suka da babbar murya kan harin da 'yan ta'adda suka kai a Ankara. Zukatanmu na tare da 'yan'uwan waɗanda suka rasu sakamakon aukuwar lamarin, kuma muna fatan samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen ƙasar a wata sanarwa da ta fitar.
"JDK na sake jaddada goyon bayanta ga Turkiyya a matakin da ta ɗauka na yaƙi da dukkan nau'ukan ta'addanci," in ji ma'aikatar.
Tun da fari, shugaban gwamnatin wucin-gadi ta Mali, Janar Assimi Goita ma ya la'anci harin.
"Muna suka da babbar murya ga harin 'yan ta'adda kan hedkwatara Masana'antar Kayan Sufurin Jiragen Sama ta Turkiyya da ke Ankara," in ji Goita a wata sanarwa.
'Cikakken goyon baya'
Da yake bayyana "cikakken goyon baya" ga Turkiyya, ya ce "Babbar abokiyar Mali ta fuskar tsaro", kuma zukatansu na tare da 'yan'uwan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Aƙalla mutane biyar ne suka mutu, yayin da 22 suka jikkata sakamakon harin ta'addanci kan Kamfanin Samar da Jiragen Sama na Turkiyya (TAI).
Yerlikaya ya ƙara da cewa an kashe maharan.
Shugaban ƙasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya bayyana harin a matsayin 'na matsorata'.
"Ina la'antar harin 'yan ta'adda a Turkiyya. Hari ne mummuna na matsorata. A madadin jama'ar Senegal, ina bayyana kauna da goyon bayanmu ga Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su da dukkan jama'ar Turkiyya," in ji Faye.
"Ina fatan samun aminci ga waɗanda suka mutu da sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata."
'Aika-Aikar matsorata'
Somalia ma ta la'anci harin, inda ta kira shi da "mummunan" harin ta'addanci.
"Wannan harin na matsorata ba Turkiyya kawai aka kai wa ba, barazanar tsaro ce ga dukkan duniya. Saboda yadda Somalia ke fuskantar irin wannan ƙalubale, tana jajanta wa Turkiyya," in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Somalia ta fitar.
Somalia ta kuma yaba da mataki nan da nan da jam'ian tsaro suka ɗauka, kuma sun yi amannar za a zartar da hukunci ga waɗanda suka yi aika-aikar.
Mogadishu na mika sakon ta'aziyya ga iyalan waɗanda ibtila'in ya shafa, kuma ƙasar na tare da jama'a da gwamnatin Turkiyya.
"Somalia na tare da Turkiyya da sauran ƙasashen duniya kan batun yaƙi da ta'addanci, tare da haɗin-kai mai tushe a al'adun bai-ɗaya da aminta da juna," in ji sanarwar da aka fitar, tana mai kira ga ƙasashen duniya da su "ƙarfafa haɗin-kai wajen yaƙi da ta'addanci."
"Tare za mu iya tabbatar da irin waɗannan aika-aika ba su raunata yunƙurinmu na kare jama'armu da wanzar da zaman lafiya ba," in ji sanarwar.