Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba. / Hoto: Reuters

2033 GMT — Isra'ila ta ce ta kashe kwamandan rundunar sojin sama ta Hezbollah a kudancin Lebanon

Isra'ila ta ce ta kashe kwamandan rundunar sojin sama ta Hezbollah a kudancin Lebanon a wani harin da ta kai ta sama, sa'o'i bayan da ta ce shi ne ya jagoranci harin da aka kai a hedkwatar sojoji a arewacin Isra'ila.

Babban mai magana da yawun rundunar sojin Isra’ila Rear Admiral Daniel Hagari ya ce Ali Hussein Barji ne ya jagoranci kai hare-hare da jiragen yaki marasa matuka a kan Isra’ila, yayin da Isra’ila da Hezbollah suke ta yaki da juna mafi muni cikin shekaru 17 da suka gabata.

1625 GMT An kashe sojojin Isra'ila tara a kwana guda

Isra’ila ta sanar da cewa an kashe mata sojoji tara a cikin kwana guda a yakin da take yi a Gaza.

Tun da farko Isra’ilar ta sanar da cewa an kashe mata sojoji hudu a yakin da take yi da Falasdinawa a kudanci da tsakiyar Gaza, sannan aka raunata shida.

Sai dai daga baya ta kara fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da kashe wasu karin sojojin nata biyar.

Zuwa yanzu an kashe sojojin Isra’ila sama da 520 tun daga soma yakin a ranar 7 ga watan Oktoba.

AA
AFP
AP
Reuters