'Yan sanda sun ce za su tabbatar an hukunta mutanen da ke da hannun a kisan dalibin,/Hoto: Reuters

Rundunar 'yan sandan Katsina da ke arewacin Nijeriya ta ce jami'anta sun kama mutum shida da ake zargi da hannu a kisan wani dalibi a Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Aliyu Abubakar-Sadiq, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Ana zargi an kashe dalibin mai suna Abubakar Nasir-Barda, sakamakon ce-ce-ku-cen da ya shafi addini sai dai 'yan sanda sun ce ba haka batun yake ba.

“Ranar 28 ga watan Satumba, 2023, wani mummunan lamari ya faru a unguwar Darawa da ke karamar hukumar Dutsinma, wanda ya hada da dalibai takwas na Jami'ar Tarayya da ke Dutsinma.

“Lamarin ya faru ne sakamakon zazzafar muhawara tsakanin daliban a kan wata daliba, wanda ya yi sanadin mutuwar dalibi daya,” in ji shi.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da cewa tuni suka kaddamar da bincike kan mutanen domin daukar matakin da ya dace.

“Mun dauki bayanai na mutanen da suka ga abin da ya faru, lamarin da zai ba mu damar gudanar da bincike kan hakikanin yadda batun ya faru da zummar yin adalci ga kowa.”

Mahaifin dalibin Nasir Ibrahim-Barda ya bukaci hukumomi su tabbatar an hukunta mutanen da suka kashe dansa, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya News Agency of Nigeria (NAN).

TRT Afrika