Shugaba Ramaphosa ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da goyon bayan mutanen da ake zalunta. Photo: AFP

Shugaban Afirka ta Kudu a ranar Litinin ya yi alƙawarin ci gaba da goyon bayan manufofi da buƙatun Falasɗinawa.

"Ba za a taɓa samun rauni ga goyon bayan da muke yi wa mutanen da ake zalunta ba," in ji Cyril Ramaphosa a wata sanarwa da ya yi a lokacin zaman majalisar dokokin ƙasar.

Ya ce ƙasarsa na goyon bayan Falasɗinu kuma za su ci gaba da goyon bayan Cuba.

"A ranar Juma'ar makon jiya, a lokacin da mambobin majalisa ke muhawara, Kotun Ƙasa da Ƙasa Mai Hukunta Manyan Laifuka ta fitar da ra'ayin bayar da shawara game da ci gaba da mamayar yankunan Falasɗinawa da Isra'ila ke yi a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, inda ta yanke hukuncin cewar wannan abu bai halasta ba a ƙarƙashin dokokin ƙasashen duniya kuma dole ne a dakatar da shi," in ji shi.

'Mikiyoyin shari'a'

Ramaphosa ya kuma ce ƙasarsa na goyon bayan buƙatar Falasɗinawa ta samun 'yanci, inda ya bayyana fatansa na cewa wannan mataki da Kotun ta ɗauka na nuni ga yadda hukumomin ƙasa da ƙasa ke ci gaba da ƙalubalantar Isra'ila kan take haƙƙoƙin Falasɗinawa da take yi.

Shugaban na Afirka ta Kudu ya ce zai gana da dukkan masana shari'ar da suka wakilci ƙasarsa a Kotun Ƙasa da Ƙasa a ƙarar da suka shigar kan a tuhumi Isra'ila da aikata kisan kiyashi.

"Waɗannan wasu ne daga jajirtattun alƙalan Afirka ta Kudu. Mikiyoyin shari'a nake kiransu, waɗanda suke aiki da ƙwarewarsu wajen ganin ƙasarmu ta kai matsayi babba a fagen shari'ar ƙasa da ƙasa," in ji shi yayin jawabi ga 'yan majalisar dokokin.

Ya kuma ce Afirka ta Kudu za ta ci gaba gwagwarmayar kawo sauye-sauye a hukumomin duniya da jagoranci irin su Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da Hukumomin Kuɗi na duniya.

TRT Afrika