Zuma ne shugaban kasar Afirka ta Kudu daga tsakanin shekarar 2009 zuwa 2018. / Photo: AFP

Kotun Kolin Afirka ta Kudu ta yanke hukunci aika tsohon Shugaban Kasar Jacob Zuma zuwa gidan yari.

A watan Yunin 2021 aka yanke wa Zuma hukuncin daurin wata 15 bisa laifin raina kotu, amma daga baya an sake shi bisa dalilan rashin lafiya a watan Satumba bayan da ya shafe wata uku a tsare.

A ranar Alhamis ne Kotun Kolin ta yanke hukuncin cewa an saki Zuma ne ba bisa ka'ida ba, don haka dole a mayar da shi gidan yari don ya kammala sauran wa'adinsa na wata 12.

Jerin daukaka kara

A watan Nuwamban 2022, Kotun Kolin ta gano cewa hukumar gidan yarin karkashin sa hannun shugabansa Arthur Fraser, ya saki Zuma ba bisa ka'ida ba yana mai kafa hujja da rashin lafiyarsa.

Gidan yarin ya kalubalanci matakin da Babbar Kotun ta dauka a watan Disamban 2021, wanda ya ba da damar a mayar da Zuma gidan yari.

Bayan da Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin Babbar Kotun a watan Nuwamban bara, sai hukumar gidan yarin ta daukaka kara a Kotun Koli.

Baki ya zo daya

A wani hukunci da dukkan alkalan suka yarda da shi, wanda Mai Shari'a Tati Makgoka ya karanta a ranar Alhamis, Kotun Kotun ta yanke hukuncin cewa matakin da aka bi na sakin Zuma bisa batun rashin lafiya ya saba wa doka, kuma dole a mayar da tsohon shugaban kasar gidan yari.

An yanke wa Zuma hukuncin daurin shekara 15 ne bayan da ya ki bin umarnin a tuhume shi kan binciken cin hanci da ake yi a shekarar 2021.

A yanzu dai hukuncin Kotun Kolin ya kawo karshen jerin daukaka kara da hukumar gidan yarin ta yi ta yi a kokarinta na ganin an wanke tsohon shugaban mai shekara 81.

Zuma ne shugaban kasar Afirka ta Kudu daga tsakanin shekarar 2009 zuwa 2018.

TRT Afrika