A yayin da masu garkuwa da mutane a Nijeriya suke ci gaba da cin karensu babu babbaka, inda suke sace kusan kowa daga ɗalibai zuwa malamai; talakawa zuwa masu kuɗi; ƙananan ’yansiyasa zuwa jami’an tsaro; ma’aikatan gwamnati zuwa alƙalai, za a iya cewa matsalar satar mutane don neman kuɗin fansa kusan babu wanda ta bari a ƙasar.
