| Hausa
'Ni ban ga irin yunwar da mutane suke magana a kai ba'
00:37
'Ni ban ga irin yunwar da mutane suke magana a kai ba'
Bayo Onanuga, Mai ba Shugaban Nijeriya Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya ce 'yan Nijeriya da dama na amfana da manufofi da sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin yanzu ta aiwatar.

Onanuga ya bayyana haka ne a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise a ranar Talata, inda ya kare manufofin shugaban ƙasa tare da yin watsi da zarge-zargen da ke cewa akwai matsananciyar wahala da rashin tsaro a faɗin ƙasar.

Mai taimaka wa shugaban ƙasar ya yi jayayya cewa ra'ayin da ake yaɗawa na cewa yunwa ta yi ƙamari a ƙasar ya samo asali ne daga wasu labarai da suka bazu jim kaɗan bayan Tinubu ya hau mulki.

Ƙarin Bidiyoyi
Sojojin Nijeriya sun kubutar da mutane daga hannun 'yanta'adda
Sojojin Isra'ila sun kama wani yaro Bafalasdine a Gabar Yamma da aka mamaye
Tagwayen girgizar kasa sun afka wa Venezuela
Isra'ila na karbar haraji daga Coci, ba kamar Daular Osmaniyya ba
Jiragen yakin Pakistan sun yi wa Shugaban Iran rakiya
Jagororin cocin Girka da Latin da ke Kudus sun ziyarci Birnin Gaza
Wani abu ya fashe a wajen ajiye iskar gas a Qatar
Matsalar daukar doka a hannu da kisan gilla
Daukakar da wakar Nana Fatima ta jawo mana
Tesla ta afka wani gida, ta yi ajalin tsohuwa mai shakara 76