| Hausa
Sojojin Nijeriya sun kubutar da mutane daga hannun 'yanta'adda
00:20
Sojojin Nijeriya sun kubutar da mutane daga hannun 'yanta'adda
Dakarun sojin Nijeriya sun kawar da wani shingen bincike da 'yanta'addan JAS/Daesh suka kafa a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya, a Ƙaramar Hukumar Biu da ke Jihar Borno, inda suka ceto fararen hula 53 tare da ƙwato motoci 8 a ranar Laraba, 24 ga watan

Wata sanarwa da Rundunar Sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa, dakarun sun ci gaba da yin dannawa, domin share hanyar da 'yan ta'addan ke bi wajen tserewa, inda suka mamaye yankin tare da gudanar da ƙarin bincike.

Dukkan mutanen da aka ceto, da motoci da kayayyakin da aka ƙwato an kai su garin Buratai cikin ƙoshin lafiya da aminci.

A halin yanzu ana yi wa fararen hulan da aka ceto rajista da kuma gwaje-gwajen lafiya, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ƙarin Bidiyoyi
Sojojin Isra'ila sun kama wani yaro Bafalasdine a Gabar Yamma da aka mamaye
Tagwayen girgizar kasa sun afka wa Venezuela
Isra'ila na karbar haraji daga Coci, ba kamar Daular Osmaniyya ba
'Ni ban ga irin yunwar da mutane suke magana a kai ba'
Jiragen yakin Pakistan sun yi wa Shugaban Iran rakiya
Jagororin cocin Girka da Latin da ke Kudus sun ziyarci Birnin Gaza
Wani abu ya fashe a wajen ajiye iskar gas a Qatar
Matsalar daukar doka a hannu da kisan gilla
Daukakar da wakar Nana Fatima ta jawo mana
Tesla ta afka wani gida, ta yi ajalin tsohuwa mai shakara 76