Nijeriya na kokarin bunƙasa ƙarfin ƙera makamai a cikin gida tare da taimakon Turkiyya, kamar yadda Ministan Tsaron kasar ya shaida wa TRT Afrika Hausa a Taron Diflomasiyya na Antalya.
Christopher Musa ya kuma ce Babban Taron Diflomsiyyar da Turkiyya ke shiryawa wanda ya samu halartar kusan mutum 5,000 daga fadin duniya, ya nuna cewa kowace ƙasa da irin matsalar da ke damunta ba Nijeriya ba kawai, kuma yana sa ran taron zai samar wa ƙasashe mafita.
