A wannan karon gwamnatin Nijar ta dakatar da manyan kafafen yaɗa labaran Faransa guda 10, ciki har da France 24, RFI da AFP, tana mai zarginsu da barazana ga tsaron ƙasa da haɗin kan al’umma.
Wannan na zuwa ne yayin da Nijar ke ci gaba da nesanta kanta daga Faransa tun bayan juyin mulkin 2023.
