Da take magana yayin wasan kwallon kafa na masu bukata ta musamman a Kano, ta bukaci gwamnati da masu hannu da shuni su kara tallafa wa masu lalura, tana mai cewa suna da baiwa da za ta iya haskawa ba kawai a Najeriya ba har ma a duniya baki daya.
Ta kuma bayyana shirye-shiryen horas da sana’o’i, tallafi da wasu tsare-tsare da ake yi domin taimaka wa masu bukata ta musamman su samu ingantacciyar rayuwa ta hanyar wasanni, ilimi da sana’o’i.
