Shugabar kamfanin Hauwa Mahmud ta ce suna gudanar da wannan sana'a ce domin rage shara da kuma tallafa wa mata wajen ganin sun dogara da kawunansu.
Ƙiyasi ya nuna cewa Nijeriya tana tara shara aƙalla tan miliyan biyu da rabi a kowace shekara, lamarin da masana suka ce yana barazana ga tsaftar muhalli da kiwon lafiya.
