| Hausa
AFIRKA
4 minti karatu
Ghana ta ba da shawarar fara amfani da kuɗin ECO a matakai tsakanin ƙasashen ECOWAS da suka shirya
Shugaba Mahama ya ce ƙoƙarin fara amfani da kuɗin ya tsaya cak tsawon shekaru da dama saboda yawan ƙasashen da ke cika ƙa’idojin daidaita tattalin arziki yana ta sauyawa.
Ghana ta ba da shawarar fara amfani da kuɗin ECO a matakai tsakanin ƙasashen ECOWAS da suka shirya
Mahama / Reuters (Wire)

Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya ba da shawarar fara amfani da kuɗin bai ɗaya na yankin Afirka ta Yamma, ECO, a matakai, inda ƙasashen da suka cika ƙa’idojin tattalin arzikin da ake buƙata za su fara amfani da shi, maimakon jiran dukkan ƙasashe 15 na ECOWAS su cika sharuddan.

A ƙarƙashin wannan shawara, ƙasashen da suka shirya haɗa tsarin kuɗinsu za su fara amfani da ECO tare da kuɗaɗen ƙasashensu, yayin da sauran ƙasashe za su iya shiga tsarin idan sun cika ƙa’idojin tattalin arzikin da ake buƙata.

“Ina da tabbacin cewa wasu daga cikinku ba a ma haife su ba lokacin da muka fara magana kan ECO, wato kuɗin bai ɗaya na Afirka ta Yamma,” in ji Mahama a ranar Talata, yayin taron ƙoli na haɗin kan Afirka ta Yamma da zuba jari (WAIIS) a birnin Freetown na Saliyo.

Ya ce ƙoƙarin fara amfani da kuɗin ya tsaya cak tsawon shekaru da dama saboda yawan ƙasashen da ke cika ƙa’idojin daidaita tattalin arziki yana ta sauyawa.

Sauyin yawan ƙasashen da suka cika sharuddan

Mahama ya tuna cewa yawan ƙasashen da suka cika sharuddan ya riƙa sauyawa tsakanin biyu, biyar, uku da bakwai. Wannan ne ya sa ya yi wuya dukkan ƙasashe 15 na Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) su cika sharuddan bai ɗaya da ake buƙata kafin fara amfani da kuɗin.

Mahama ya ce shi da shugaban Saliyo, Julius Maada Bio, sun gabatar da shawara a taron ƙolin ECOWAS na baya domin warware wannan tsaiko, ta hanyar bai wa ƙasashen da suka shirya damar fara haɗa tsarin kuɗinsu.

A ƙarƙashin tsarin da ake shirin aiwatarwa, ECO zai sauƙaƙa biyan kuɗin cinikayya tsakanin ƙasashen da suka shiga tsarin, ba tare da sai an bi ta dalar Amurka ba, yayin da kuɗaɗen ƙasashen za su ci gaba da kasancewa a amfani.

Shugaban na Ghana ya kuma bayyana ƙarancin ababen more rayuwa na sufuri da jigilar kayayyaki a matsayin babban cikas ga faɗaɗa cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka, duk da ci gaban da aka samu ƙarƙashin Yarjejeniyar Cinikayya Marar Shinge ta Nahiyar Afirka (AfCFTA).

Ya ce cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka ta ƙaru daga kusan kashi 11 cikin 100 a lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar AfCFTA zuwa kusan kashi 15 cikin 100. Sai dai ya ce wannan bai kai yadda cinikayya ke gudana tsakanin ƙasashen Tarayyar Turai ba, inda take tsakanin kashi 50 zuwa 60 cikin 100.

“Amma babban cikas ɗin shi ne harkar sufuri da jigilar kayayyaki. Shin muna da tashoshin jiragen ruwa? Muna da layukan dogo? Muna da hanyoyi?” in ji shi.

Jinkirin aiwatar da manyan ayyukan haɗin gwiwar yankin

Mahama ya kawo aikin titin Lagos zuwa Abidjan da aka daɗe ana jinkirin aiwatarwa a matsayin misalin yadda ake tafiyar hawainiya wajen bunƙasa ababen more rayuwa na yankin. Ya tuna cewa an fara gabatar da aikin ne a ƙarshen shekarun 1990, lokacin da yake ƙaramin minista.

“Yau shekaruna sun kusa 70, amma har yanzu aikin titin Abidjan zuwa Lagos yana kan takarda,” in ji shi, yana mai cewa wannan jinkiri ya nuna cewa haɗin kan yankin bai wuce buri da maganganu ba.

Ya buƙaci shugabannin Afirka ta Yamma su wuce matakin sanar da manufofi kawai, su kuma hanzarta aiwatar da ayyukan samar da ababen more rayuwa da za su inganta zirga-zirgar mutane da kayayyaki a yankin.

Mahama ya kuma yi kira da a samar da ingantaccen tsarin hanyoyin mota na bai ɗaya, da kafa wuraren binciken iyakoki na bai ɗaya, tare da kawar da shingayen binciken ’yan sanda da jami’an tsaro da ba su da muhimmanci, domin sauƙaƙa cinikayya tsakanin ƙasashe.

Ya ce kammala aikin titin Lagos zuwa Abidjan zai zama ginshiƙi wajen faɗaɗa hanyoyin sufuri na yankin zuwa Dakar, tare da ƙarfafa haɗin kan tattalin arzikin Afirka ta Yamma.