| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Tinubu ya yi wa mutum 78 afuwa bayan kama su da laifin kai hari ga ayarin motocinsa a Abuja
An kama waɗanda ake zargin ne bayan wani hari da aka kai wa ayarin motocin shugaban ƙasa ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, jim kaɗan bayan ya idar da sallar Juma’a a wani masallaci da ke unguwar Garki a Abuja.
Tinubu ya yi wa mutum 78 afuwa bayan kama su da laifin kai hari ga ayarin motocinsa a Abuja
Tinubu / Nigeria Presidency

Rundunar ’yansandan Babban Birnin Tarayya (FCT) ta ce tana shirye-shiryen sakin mutum 78 da aka kama bisa zargin kai hari ga ayarin motocin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Bola Tinubu, a Abuja, bayan umarnin shugaban ƙasar na yi musu afuwa.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, kakakin rundunar ’yan sandan FCT, Josephine Adeh, ta ce fadar shugaban ƙasa ta bayar da umarnin gargadin waɗanda ake zargin tare da sakin su.

Ta ƙara da cewa a halin yanzu ana kammala matakan da suka dace domin sakin mutanen.

An kama waɗanda ake zargin ne bayan wani hari da aka kai wa ayarin motocin shugaban ƙasa ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, jim kaɗan bayan ya idar da sallar Juma’a a wani masallaci da ke unguwar Garki a Abuja.

Rahotanni sun ce wasu mutane sun yi wa ayarin motocin shugaban ƙasar luguden duwatsu da wasu abubuwa masu haɗari yayin da yake barin wurin, lamarin da ya lalata wasu motoci tare da jikkata jami’an tsaro.

’Yan sanda sun ce wani haɗin gwiwar jami’an tsaro ya gaggauta mayar da martani kan lamarin, yayin da samamen da aka gudanar daga baya bisa bayanan sirri a yankin ya kai ga kama wasu ƙarin mutane, wanda ya sa adadin waɗanda aka kama ya kai 78.

A cikin sanarwar, rundunar ’yan sandan ta ce tana aiwatar da sakin waɗanda ake zargin ne bisa umarnin fadar shugaban ƙasa.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan ’yan sandan Babban Birnin Tarayya, Ahmed Sanusi, ya yi gargaɗi kan aikata tashin hankali, tayar da hargitsi da lalata dukiyoyin jama’a.

Ya buƙaci jam’iyyun siyasa, ’yan siyasa da magoya bayansu da su rungumi tattaunawa da hulɗa cikin lumana, yayin da shirye-shiryen babban zaɓen Nijeriya na 2027 ke ƙara ƙamari.