| Hausa
KIMIYYA DA FASAHA
2 minti karatu
Italiya ta ci Meta tarar dala miliyan 880 bisa shiga hotunan wayoyin mutane ba tare da izini ba
Hukumar ta gano cewa Facebook na neman izini guda ɗaya na bai ɗaya domin samun damar shiga kundin hotunan masu amfani da manhajar, ba tare da bayyana musu cewa hakan zai bayar da damar amfani da wannan fasali ba.
Italiya ta ci Meta tarar dala miliyan 880 bisa shiga hotunan wayoyin mutane ba tare da izini ba
Tarar ta biyo bayan wani bincike da hukumar kare bayanan sirri ta Italiya ta gudanar kan wani sabon fasali da Facebook ya ƙaddamar a shekarar 2023. / Reuters (Wire)

Hukumomin kula da harkokin sadarwa da bayanan sirri na Italiya sun ci tarar kamfanin Meta, mamallakin Facebook, har Euro miliyan 805 kwatankwacin dala miliyan 880, bisa zargin samun damar duba hotunan masu amfani da manhajar ba tare da samun sahalewar su ta musamman ba.

Hukumar kare bayanan sirri ta ƙasar a ranar Asabar ta bayyana cewa, ta hanyar manhajar Facebook da ake amfani da ita a wayoyin Android, Meta ta samu damar shiga hotuna, bidiyoyi da bayanan da ke tattare da su na masu amfani da manhajar a Italiya ba tare da samun izininsu na musamman ba, ko kuma yi musu cikakken bayani kan hakan.

Tarar ta biyo bayan wani bincike da hukumar kare bayanan sirri ta Italiya ta gudanar kan wani sabon fasali da Facebook ya ƙaddamar a shekarar 2023.

Fasalin, mai suna “Get suggestions from your gallery while browsing Facebook”, yana bai wa manhajar damar ba masu amfani da ita shawarar hotuna da bidiyoyin da ke cikin wayoyinsu domin su wallafa a Facebook.

Hukumar ta gano cewa Facebook na neman izini guda ɗaya na bai ɗaya domin samun damar shiga kundin hotunan masu amfani da manhajar, ba tare da bayyana musu cewa hakan zai bayar da damar amfani da wannan fasali ba.

Ta kuma gano cewa ana kunna fasalin ne kai tsaye ba tare da neman ƙarin izini ba, kuma wannan izinin na iya bai wa manhajar damar shiga dukkan hotuna da bidiyoyin da ke cikin wayar Android, har da bayanan da ke tattare da su.

An fara gudanar da binciken ne a watan Yulin 2025 bayan wata ƙungiyar kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki ta shigar da ƙara.

Hukumar Italiya ta yanke hukuncin cewa Meta ta karya dokokin kare bayanan sirri ta hanyar shiga hotunan masu amfani da manhajar ba tare da samun cikakken izininsu ba. Ta kuma yi watsi da hujjar kamfanin cewa ya kamata ƙasar Ireland ce ta gudanar da binciken.

Hukumar ta bai wa Meta wa'adin kwanaki 60 domin samar da wani tsari na neman izini na musamman daga masu amfani da manhajar, tare da kashe wannan fasali ta yadda ba zai riƙa kunnawa kai tsaye ba.

Ta ce an ƙayyade tarar ne bisa girman laifin da aka aikata, wanda ya shafi kusan masu amfani da wayoyin Android miliyan 20 a Italiya.