| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
An kashe mutum biyar ciki har da mutum biyu da ake zargi da kai hari Cibiyar Musulunci a San Diego
Masu bincike suna kallon lamarin a matsayin wanda zai iya kasancewa laifin nuna ƙiyayya, yayin da Trump ya bayyana harbin a matsayin wani "mummunan lamari".
An kashe mutum biyar ciki har da mutum biyu da ake zargi  da kai hari Cibiyar Musulunci a San Diego
Wurin da aka bayar da rahoton harbe-harbe a Cibiyar Musulunci ta San Diego, California. / Reuters

An kashe mutane biyar a harin bindiga a Cibiyar Musulunci a San Diego, ciki har da mutum biyu da ake zargi su ne maharan, yayin da 'yansanda suka ce suna ɗaukar lamarin a matsayin yiwuwar laifi na nuna ƙiyayya.

Hukumomi sun ce wasu matasa biyu da ake zargi sun buɗe wuta a cibiyar Musulunci a San Diego a ranar Litinin, inda suka kashe maza uku kafin su kashe kansu.

An ce wani jami'in tsaro yana cikin waɗanda aka kashe a masallacin, in ji shugaban 'yansandan San Diego, Scott Wahl.

''Abin da muka sani a wannan lokaci shi ne, akwai manya maza uku da suka mutu,' in ji Shugaban 'Yansanda na San Diego Scott Wahl, yana nuni ga waɗanda suka mutu, sannan ya ƙara da cewa mutum biyu da ake zargin su suka kai harin su ma sun mutu.

Yayin da yake magana a taron manema labarai bayan da hukumomi suka bayyana a baya cewa an kawar da barazanar, Wahl ya ce ɗaya daga cikin mamatan jami'in tsaro ne da yake aiki a cibiyar.

Saboda wurin da Cibiyar Musulunci take, muna ɗaukar wannan a matsayin yiwuwar laifi na ƙiyayya har sai an tabbatar da akasin haka, kuma a wannan mataki za mu yi aiki tare da FBI kafada-da-kafada don tabbatar da mun haɗa dukkan abubuwan da muke buƙata don binciken,' in ji shi.

Gwamnan California, Gavin Newsom, ya ce yana da masaniya game da harbin a masallacin, kuma yana samun sabbin bayanai daga jami'an tsaro yayin da ma'aikatan gaggawa ke aiki a wurin.

''Mummunan lamari''

Cibiyar Musuluncin a Clairemont, yankin da jama’a ke zama kuma ake kasuwanci a San Diego, ita ce masallaci mafi girma a gundumar San Diego, a cewar shafinta na intanet.

Shugaba Donald Trump ya bayyana harbin a matsayin 'mummunan lamari'.

'Suna bayar da bayanai a kai... kuma lamari ne mai muni. An ba ni wasu sabbin bayanai na farko, amma za mu koma mu nazarce shi sosai,' kamar yadda Trump ya faɗa wa 'yanjarida a Fadar White House.

A gefe guda kuma, Daraktan Cibiyar Musuluncin ta San Diego, Taha Hassane, ya shaida wa 'yanjarida cewa kai hari kan wurin ibada abin kunya ne ƙwarai.

'Ba mu taɓa fuskantar irin wannan masifa ba a baya,' a cewar Hassane.

Hukumar Majalisar Hulɗar Amurka da Musulunci (CAIR) reshen San Diego ta yi suka kan harin.

'Allah ya ba shi mafi ɗaukakar daraja a Aljanna kuma ya kare kowa daga sharri. Bai kamata a ce wani yana fargabar wani abu zai same shi ba, yayin da yake halartar ibada ko karatu a makarantar firamare,' CAIR ta faɗa a shafin X.

Cibiyar Musuluncin tana da mambobi fiye da 5,000, a cewar shafinta na intanet.

Harabar cibiyar na ɗauke da Makarantar Al Rashid, wacce ke koyar da addini da harsuna.

Cibiyar ta bayyana cewa burinta shi ne tallafa wa al'umma tare da yin aiki da jama'a baki ɗaya don taimakon marasa galihu, da inganta ilimi, da bayar da gudunmawa ga ci-gaban Amurka.

Rumbun Labarai
'Yan Afirka da suka je Indiya neman lafiya na cikin mutum 21 da gobarar hotal ta kashe a New Delhi
Trump ya tattauna yarjejeniyar Iran da masu taimaka masa, amma an ce bai yanke hukuncin ƙarshe ba
Saudiyya ta sanar da kammala Hajjin 2026 lafiya inda alhazai miliyan 1.7 suka yi ibadah
Majalisar Faransa ta kaɗa ƙuri'ar gyara dokokin bauta na zamanin mulkin mallaka
Trump ya yi barazanar kai wa ƙasashe 15 hari a lokacin mulkinsa: CNN
A cikin hotuna: Yadda Musulamai a fadin duniya suka yi Idin Babbar Sallah
Miliyoyin Musulmai sun taru a kan Dutsen Arfa yayin da aka kai ƙololuwar Aikin Hajji
Fafaroma Leo XIV ya nemi afuwa kan rawar da Cocin Katolika ya taka a cinikin bayi tsakanin nahiyoyi
Alhazai sun fita Mina: Kimanin Musulmai miliyan 2 sun fara Aikin Hajjin 2026
Trump ya ce tattaunawar Iran 'ta yi armashi', amma ba za a janye takunkumi ba sai an gama yajejeniya
An kashe danbindiga bayan tunkarar wajen bincike na White House, in ji hukumar tsaron Secret Service
Saudiyya na amfani da jirage marasa matuka da fasahar AI  don sanya idanu kan ayyukan Hajji
Trump da Netanyahu sun samu saɓani yayin zazzafar tattaunawa ta waya kan makomar yaƙin Iran — rahoto
Rasha da China sun ƙarfafa haɗin gwiwar dabarun yaki da sabbin yarjejeniyoyi
Ana ta ƙoƙarin gano ɓeran da ya janyo ɓullar cutar Hantavirus mai kisa
Mata manya da yara na Rohingya da ke jihar Rakhine na fuskantar tsananin fyaɗe
FBI za ta bayar da ladar $200,000 ga wanda ya taimaka aka kama wata sojar Amurka da ta koma Iran
Mbappe na gaba-gaba a tawagar Faransa ta Gasar Kofin Duniya; an sauƙe Camavinga, Chevalier
Xi da Trump sun amince Mashigar Hormuz ta ci gaba da kasancewa a buɗe
Amurka ta ɗauke wa magoya bayan tawagogin Afirka biyar biyan $15,000 na jinginar biza