| Hausa
DUNIYA
4 minti karatu
Trump da Netanyahu sun samu saɓani yayin zazzafar tattaunawa ta waya kan makomar yaƙin Iran — rahoto
Rahortanni sun ce Firaministan Isra'ila ya dage kan a ci gaba da zafafa yaƙi, yayin da shugaban Amurka ya dage kan cewa za a iya cim ma yarjejeniya, kamar yadda rahotannin kafofin watsa labarai suka bayyana.
Trump da Netanyahu sun samu saɓani yayin zazzafar tattaunawa ta waya kan makomar yaƙin Iran — rahoto
Rahotannin kafofin yada labaran Amurka sun ce Trump da Netanyahu suna da sabani kan hanyar da za a bi game da Iran. (Hoto: FILE) / AP

Shugaban Amurka Donald Trump da Firaminista Isra’ila Benjamin Netanyahu sun yi wata zazzafar tattaunawa ta waya a ranar Talata, wadda ta nuna manyan bambance-bambance kan yadda za a tafiyar da yaƙin da ke ci gaba da gudana da Iran, in ji rahotannin kafofin watsa labarai na Amurka.

Kiran ya biyo bayan bayanin da Trump ya yi wa Netanyahu a wata tattaunawa a ranar Lahadi cewa yana shirin ƙaddamar da sabbin jerin hare-hare kan Iran a farkon makon, wanda za a kira Operation Sledgehammer, kamar yadda rahotannin CNN na baya bayan nan suka nuna.

Sai dai, daga baya Trump ya sanar da ɗage harin da aka shirya kai wa a ranar Talata, bayan bukatun wasu manyan ƙawayen Amurka a yankin Tekun Fasha, ciki har da Qatar, da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.

A kwanakin da suka biyo baya, waɗannan ƙasashe sun shiga cikin ƙoƙarin sasanci mai zurfi tare da jami’an Fadar White House da Pakistan domin tsara wata hanya ta dawo da tattaunawar diflomasiyya, in ji masu masaniya kan tattaunawar.

A yayin kiran waya na kusan awa guda a ranar Talata, Netanyahu ya shaida wa Trump cewa jinkirta harin wani kuskure ne kuma ya buƙaci ya ci gaba da aikin soja kamar yadda aka tsara a baya, in ji wani jami’in Amurka da wata majiya ta Isra’ila.

"Bambancin ra'ayi ya bayyana sosai, Trump yana son ganin ko za a iya cim ma yarjejeniya, amma Netanyahu yana tunanin wani abu daban," kamar yadda wani jami'in Isra'ila ya faɗa wa CNN.

Axios ne ya fara bayar da rahoton zazzafar wannan kiran waya.

Bambance-bambance tsakanin Washington da Tel Aviv

"Muna cikin matakai na ƙarshe kan batun Iran. Za mu ga abin da zai faru," kamar yadda Trump ya faɗa wa 'yanjarida a ranar Laraba. "Ko za mu cim ma yarjejeniya ko kuma za mu yi wasu abubuwa waɗanda ka iya zama masu tsanani. Amma da fatan hakan ba zai faru ba."

Netanyahu, wanda kullum yake goyon bayan ɗaukar matsayi mai tsauri na soji kan Tehran, ya ƙara fusata sakamakon jinkirin, wanda yake ganin yana ƙarfafa matsayin Iran kawai.

Damuwar da na kusa da Netanyahu ke ciki ta ƙaru, inda manyan jami'an Isra'ila ke matsa lamba sosai don a sake kai hare-hare, kuma suna bayyana fushinsu kan abin da suke kira jinkirin diplomasiyyar Iran, in ji wani tushe na Isra'ila ga CNN.

Ba wannan ne karon farko da bambance-bambance suka bayyana tsakanin Washington da Tel Aviv ba.

A baya jami'an Amurka sun amince cewa ba a koyaushe ƙawayen suke da manufofi ɗaya game da Iran ba.

Lokacin da aka tambaye shi a ranar Laraba game da tattaunawarsa da Netanyahu, Trump ya tabbatar da cewa shi ne mai faɗa a ji kan batun, yana cewa, "Zai yi duk abin da nake so ya yi."

Trump ya ci gaba da bin hanyar diflomasiyya zuwa yanzu, yana bayyana cewa abubuwan da ke faruwa game da Iran suna "kan iyaka" kuma bai wa tattaunawa wasu ƙarin kwanaki kaɗan na iya ceton rayuka.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya tabbatar a ranar Laraba cewa Tehran da Washington har yanzu suna musayar saƙonni ta hanyar Pakistan.

Duk da haka, har yanzu akwai muhimman ɓangarorin da ake da giɓi tsakanin bangarorin biyu. Iran ba ta sassauta bukatunta na asali ba, yayin da har farkon wannan makon ba a warware batutuwan da suka shafi shirin nukiliyarta da kadarorinta da aka sanya wa takunkumi ba, in ji wata majiya ta yankin.

Trump ya ci gaba da barin yiwuwar amfani da soja a buɗe, yana gargadin cewa, "Idan ba mu samu amsoshin da suka dace ba, abubuwa za su tafi da sauri. Dukkanmu mun shirya bazama."