| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Majalisar Faransa ta kaɗa ƙuri'ar gyara dokokin bauta na zamanin mulkin mallaka
'Yan masajalisar sun kaɗa ƙuri'ar soke dokokin da suka shafi bauta a wuraren da Faransa ta yi wa mulki mallaka
Majalisar Faransa ta kaɗa ƙuri'ar gyara dokokin bauta na zamanin mulkin mallaka
Wata mace tana gabatar da Gwoka, wani nau'in kiɗa na gargajiya, a Cibiyar Caribbean ta Nuna Fasaha da Tunawa da Bauta da Fataucin Bayi da ke Pointe-à-Pitre. / AFP

Majalisar wakilai ta Faransa ta kaɗa kuri'a da gagarumin rinjaye domin soke wasu dokokin daruruwan shekaru da suka gabata wadanda suka halatta bauta a kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, abin da ya nuna wani mataki da ke nuna alamar damuwa da kuma fuskantar abubuwan da suka faru a tarihin mulkin mallakar kasar.

Wakilai a Majalisar Dokoki sun amince da ƙudirin da ya amince da soke dokar “Code Noir,” jerin wasu dokoki na ƙarni na 17 da na 18 da suka tsara bauta a duka fadin yankunan da Faransa ta yi wa mulkin mallaka. Matakin ya samu amincewar ‘yanmajalisa 250, yayin da ko da ɗan majlisa ɗaya bai nuna rashin amincewa ba.

Duk da cewa an soke bauta a kasar Faransa tun a shekarar 1848, ba a soke waɗannan dokokin ba a hukumance sai yanzu.

Har yanzu dokar tana buƙatar amincewar Majalisar Dattijai kafin ta zama doka. Ba a tsara lokacin kaɗa ƙuri'a a Majalisar Dattijai ba tukuna.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya goyi bayan soke dokar a farkon wannan watan, yana cewa ci gaba da kasancewar waɗannan dokoki bai dace da ƙimar Jamhuriyar Faransa ba.

'Code Noir'

Yayin da yake jawabi a Fadar Élysée a lokacin wani biki da aka shirya domin cika shekaru 25 tun bayan da Faransa amince da bauta da cinikin bayi a matsayin laifi na cin zarafin ɗan’adam, Macron ya ce dole Faransa ta fuskanci tarihinta da gaskiya kuma ta amince cewa ba za a iya gyara wahalhalun da bauta suka haifar gaba ɗaya ba.

Shugaban Majalisar Wakilai Yael Braun-Pivet, ta yi maraba da ƙuri'ar a wani rubutu a X, a matsayin shawara da aka yanke saboda mutunta “ɗan’adam, da daidaito, da bin tsarin duniya baki ɗaya.'

“'Code Noir' ta nuna rashin mutunta ɗan’adam a cikin dokoki,” kamar yadda Braun-Pivet ta rubuta. “Majalisar Wakilai ta soke ta a hukumance a yau ba tare jayayya ba.”

Ta ƙara da cewa dole Faransa ta 'bayyana ba tare da gogewa ba, ta yarda don ta isar,' yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar tarihinta 'da fahimta' shekaru 25 bayan dokar Taubira ta amince da bauta a matsayin laifi na cin zarafin ɗan’adam.

Muhawarar game da 'Code Noir' ta taso ne a daidai lokacin da ake ƙara samun kiraye-kiraye daga masu rajin canji da 'yan majalisa da suke tilasta wa Faransa magance gadon bauta, da mulkin mallaka da wariyar launin fata.