| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Amurka ta ɗauke wa magoya bayan tawagogin Afirka biyar biyan $15,000 na jinginar biza
Ƙasashen Afirka biyar da suka samu shiga gasar cin kofin duniya suna cikin ƙasashen da ake buƙatar 'yan ƙasashensu su biya kudin jingina na biza: Aljeriya da Cape Verde da Ivory Coast da Senegal da kuma Tunisiya.
Amurka ta ɗauke wa magoya bayan tawagogin Afirka biyar biyan $15,000 na jinginar biza
TOSOHON HOTO: Magoya bayan tawagar ƙwallon ƙafar Senegal a cikin wani filin wasa a lokacin gasar cin kofin Afirka da aka yi a Maroko. / Reuters

Amurka ta bayyana ranar Laraba cewa za ta sauƙaƙa tsarinta na buƙatar biyan kuɗaɗen jingina ga masu neman izinin shiga ƙasarta ga wasu magoya bayan tawagogin ƙasashe a gasar cin kofin duniya.

A ƙarƙashin ɗaya daga cikin tsare-tsaren Shugaba Donald Trump domin daƙile shiga ƙasar, Amurka ta fara neman mutane daga ƙasashe hamsin su miƙa kuɗi daga $5,000 zuwa $15,000 domin samun bizar shiga Amurka, kuɗin da za a iya mayar musu da zarar sun koma ƙasashensu.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce za ta ɗauke kuɗaɗen jingina ga ‘yan tawagogin da za su fafata a wasannin gasar cin kofin duniya tare da magoya baya daga ƙasashen da za su fafata da suka riga suka samu tikiti kuma suka yi rajista wa tsarin ba da fifiko da aka tsara wa ba da biza.

Ƙasashen Afirka biyar da suka samu shiga gasar cin kofin duniyar suna cikin ƙasashen da ‘ya’yansu ke da buƙatar biyan kuɗaɗen jingina na biza : Aljeriya da Cape Verde da Ivory Coast da Senegal da Tunisiya.

"Mun duƙufa wajen mayar da hankali kan ƙarfafa tsaron ƙasar Amurka yayin ba da damar damar tafiya da ta dace da doka game da gasar cin kofin duniya da ke tafe," a cewar Mora Namdar, mataimakiyar sakataren harkokin wajen ƙasar da ke lura da batutuwa na jadakanci.

‘Gasar cin kofin duniya ta FIFA da ta fi ko wace’

Ta ce gwamnatin Trump tana son ta shirya "gasar cin kofin duniya ta FIFA mafi ƙayartawa da kuma mafi girma a tarihi."

"Sanarwar yau daga ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta kuma nuna haɗin gwiwar da muke da gwamnatin Amurka da kwamiti na musamman na fadar White House kan gasar cin kofin duniya ta FIFA domin samar da wani taron duniya mai cike da nasara da zai kafa tarihi wanda kuma ba za a manta da shi ba," kamar yadda wani mai magana da yawun hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ya bayyana a wata sanarwa.

Gwamnatin Trump ta kuma faɗaɗa bincike sosai kan baƙi daga ƙasashen yammacin duniya da ke ƙawayen ƙasar , tana mai buƙatar su su bai wa gwamnatin Amurka damar duba ababen da suka wallafa a shafukansu na sada zumunta .

Gasar cin kofin duniya , wadda za a fara ranar 11 ga watan Yuni, ƙasashen Kanada da Meziko da Amurka ne za su karɓi baƙuncinta tare.

Rumbun Labarai
Majalisar Faransa ta kaɗa ƙuri'ar gyara dokokin bauta na zamanin mulkin mallaka
Trump ya yi barazanar kai wa ƙasashe 15 hari a lokacin mulkinsa: CNN
A cikin hotuna: Yadda Musulamai a fadin duniya suka yi Idin Babbar Sallah
Miliyoyin Musulmai sun taru a kan Dutsen Arfa yayin da aka kai ƙololuwar Aikin Hajji
Fafaroma Leo XIV ya nemi afuwa kan rawar da Cocin Katolika ya taka a cinikin bayi tsakanin nahiyoyi
Alhazai sun fita Mina: Kimanin Musulmai miliyan 2 sun fara Aikin Hajjin 2026
Trump ya ce tattaunawar Iran 'ta yi armashi', amma ba za a janye takunkumi ba sai an gama yajejeniya
An kashe danbindiga bayan tunkarar wajen bincike na White House, in ji hukumar tsaron Secret Service
Saudiyya na amfani da jirage marasa matuka da fasahar AI  don sanya idanu kan ayyukan Hajji
Trump da Netanyahu sun samu saɓani yayin zazzafar tattaunawa ta waya kan makomar yaƙin Iran — rahoto
Rasha da China sun ƙarfafa haɗin gwiwar dabarun yaki da sabbin yarjejeniyoyi
Ana ta ƙoƙarin gano ɓeran da ya janyo ɓullar cutar Hantavirus mai kisa
An kashe mutum biyar ciki har da mutum biyu da ake zargi  da kai hari Cibiyar Musulunci a San Diego
Mata manya da yara na Rohingya da ke jihar Rakhine na fuskantar tsananin fyaɗe
FBI za ta bayar da ladar $200,000 ga wanda ya taimaka aka kama wata sojar Amurka da ta koma Iran
Mbappe na gaba-gaba a tawagar Faransa ta Gasar Kofin Duniya; an sauƙe Camavinga, Chevalier
Xi da Trump sun amince Mashigar Hormuz ta ci gaba da kasancewa a buɗe
Wani sanatan Amurka ya fada wa Majalisar Dattawa cewa ƙasar ta yi asarar jirage 39 a yakin Iran
Ƙarancin abinci: Toshe Mashigar Hormuz na barazana ga mutum miliyan 45 a duniya in ji MDD
WHO ta ce duniya ba ta fuskantar barazana bayan ɓullar cutar hantavirus a wani babban jirgin ruwa