| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Liverpool ta kori kocinta Arne Slot bayan rashin kataɓusa a kakar wasannin nan
Arne Slot ya ya yi ƙoƙari a kakarsa ta farko inda Liverpool ta lashe kofin Firimiya, amma ta sha fama a shekarara tabiyu, inda kulob din ta kare a matsayi na biyar.
Liverpool ta kori kocinta Arne Slot bayan rashin kataɓusa a kakar wasannin nan
Arne Slot ya maye gurbin Jurgen Klopp a matsayin kocin Liverpool a shekarar 2024. / Reuters

Liverpool ta raba gari da Arne Slot, in ji kulob din na Merseyside a ranar Asabar, bayan mai horarwar wanda ya lashe kofin Firimiya a kakar farko ya gaza taka rawar gani ya kammala a matsayi na biyar.

Slot, ya maye gurbin Juergen Klopp a 2024, kuma dan kasar Holland ɗin ya shana a kakar farko lokacin da Liverpool ta lashe kofin Firimiya.

Sai dai kakarsa ta biyu a Liverpool ta koma daga kokarin kare kofin zuwa yunkurin neman gurbin gasar Zakarun Turai cikin wahala, yayin da ya kasa lashe kowane kofi na cikin gida, abin da ya nuna koma baya mai girma ga zakarun da ke riƙe da kambin.

A cikin wata sanarwa, Liverpool ta ce: "Babu shakka wannan shawara ce mai wahala gare mu a matsayin kulob. Gudunmawar da Arne ya bayar ga Liverpool FC a lokacin da yake tare da mu ta kasance mai muhimmanci, mai ma'ana kuma — mafi muhimmanci ga magoya baya da mu kanmu — mai nasara."

'Canji ya zama dole'

”Hakan ya bayyana lokacin da ya amince ya karbi ragamar horarwa, lokacin da ya jagorance mu zuwa lashe kofin Firimiya, amma kuma a gaba daya kakar da ta gabata, ya fuskanci manyan ƙalubale da nauye-nauye.

“A lokaci guda, dukkanmu mun yarda cewa sauyi ya zama dole, domin kulob din ya ci gaba da yin gaba. Kuma, ya kamata a sake jaddada cewa wannan ba yanke shawara ba ce da aka yi cikin sauki, mataki ne mai wahala.”

Liverpool ta ce ana cikin aikin naɗa wanda zai maye gurbinsa, inda rahotannin kafafen watsa labarai ke alakanta Andoni Iraola da wannan mukami, bayan ɗan kasar Sifaniya ɗin ya jagoranci Bournemouth zuwa matsayi na shida a gasar lig inda suka samu damar shiga gasar Europa a karon farko.