| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Kofin Duniya na 2026: FIFA za ta fito da sabuwar dokar da ake wa lakabi da "A-kori-Arsenal"
Salon riƙe ƙwallo da ake kira da “Set piece”, wato dabarar tsayar da wasa don saita ‘yanwasa a fili yadda za su ciyo ƙwallo, ya zama wata babbar hanyar cin ƙwallo musamman a gasar Firimiya.
Kofin Duniya na 2026: FIFA za ta fito da sabuwar dokar da ake wa lakabi da "A-kori-Arsenal"
Za a bude Gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 ranar 11 ga Yunin 2026 / Reuters

Yayin da ya rage kwanaki 10 a buɗe gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026, rahotanni na cewa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniyar ta shirya ƙaddamar da wata sabuwar dokar wasannin ƙwallo.

Sabuwar dokar da ake wa laƙabi da “A-kori-Arsenal” na cikin jerin sabbin dokoki da aka yi wa sauyi, kuma an yi amfani da ƙasar Ingila don yin misalin yadda dokar za ta yi aiki.

Salon riƙe ƙwallo da ake kira da “Set piece”, wato dabarar tsayar da wasa don saita ‘yanwasa a fili yadda za su ciyo ƙwallo, ya zama wata babbar hanyar cin ƙwallo musamman a gasar Firimiya.

Hakanan hukumomin FIFA da na IFAB, mai kula da dokokin buga wasanni, suna ƙoƙarin yaƙar yin ture da tunkuɗe yayin amfani da wannan dabarar.

Dokar za ta fara aiki yayin gasar Kofin Duniya, sannan daga bisani a ɗabbaƙa ta a a sauran manyan gasanni daga farkon Yulin 2026.

An kafa misali da ƙwallon da Ingila ta ci Uruguay a wasansu na sada-zumunta a Maris, inda ɗanwasan Ingila Ben White, ya ci ƙwallo yayin da ‘yanwasan bayan Ingila, Adam Wharton da Harvey Barnes suka tare ‘yanwasan bayan Uruguay yayin bugun kwana.

Masu sharhi kan wasanni na ganin cewa sabuwar dokar za ta yi babban tasiri kan gasar Firimiya ta Ingila, inda salon wasan ya yi suna, musamman ganin yadda Arsenal ta ci jimillar ƙwallo 25 da wannan dabarar.

Hasali ma, wannan ne ya sa ake wa dokar laƙabi da “a-kori-Arsenal” saboda ƙaurin suna a wannan fagen.

Ranar 11 ga Yuni ne za a buɗe gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 a ƙasashen Amurka, Canada, da Mexico.