| Hausa
WASANNI
2 minti karatu
Ghana ta bayyana sunayen 'yanwasa 26 da za su buga mata gasar Cin Kofin Duniya
Za a fara gasar Cin Kofin Duniya ne a Amurka, Canada, da Mexico a ranar 11 ga watan Yuni, Ghana zata fafata da Panama a wasanta na farko a rukunin L bayan kwanaki shida da fara gasar. Sauran kasashen da ke cikin rukunin sun hada da Ingila da Croatia.
Ghana ta bayyana sunayen 'yanwasa 26 da za su buga mata gasar Cin Kofin Duniya
Ghana tana rukunin L tare da Ingila da Canada da Croatia / Reuters

Ɗanwasan gaba na ƙungiyar Manchester City, Antoine Semenyo, da kuma tsohon ɗanwasan tsakiyar Arsenal, Thomas Partey, suna cikin jerin sunayen 'yanwasan 26 da koci Carlos Queiroz ya zaɓa domin wakiltar Ghana a Gasar Kofin Duniya.

Tawagar ta Ghana za ta fafata da takwararta ta Wales a birnin Cardiff ranar Talata a wasan sada zumunta, kafin daga bisani su garzaya Arewacin Amurka domin halartar Gasar Kofin Duniya, wanda shi ne karo na biyar da ƙasar take halartar gasar.

Daga cikin 'yanwasan tsakiya akwai Partey mai shekaru 32 da ke buga wa Villarreal wasa, wanda ake sa ran zai gurfana gaban kotu a Birtaniya nan gaba kaɗan kan zargin fyaɗe da cin zarafin mata, ko da yake ya musanta laifin.

Tsohon ɗanwasan gaba na kungiyar Leicester City, Jordan Ayew, shi ne zai jagoranci ƙungiyar ta Black Stars a matsayin kyaftin, yayin da ɗanwasan gefe na Tottenham, Mohammed Kudus, ba zai samu damar buga gasar ba saboda rashin lafiya.

Semenyo mai shekaru 26 ya zura ƙwallaye 11 a wasanni 27 da ya buga wa City bayan ya koma can daga Bournemouth a watan Janairu kan kudi fam miliyan £62.5.

Za a fara Gasar Kofin Duniyar ne a ƙasashen Amurka, Canada, da kuma Mexico a ranar 11 ga watan Yuni, inda Ghana za ta fafata da Panama a wasanta na farko a rukunin L bayan kwanaki shida da fara wasan. Sauran ƙasashen da ke cikin rukunin da ake ganin za a fafata sun haɗa da Ingila da Croatia.

Jerin Sunayen 'Yan Wasan Ghana

Masu Tsaron Gida: Benjamin Asare, Lawrence Ati-Zigi da Joseph Anang.

‘Yan Baya: Baba Abdul Rahman, Gideon Mensah, Marvin Senaya, Alidu Seidu, Abdul Mumin, Jerome Opoku, Jonas Adjetey, Kojo Oppong Peprah da Derrick Luckassen.

'Yan Wasan Tsakiya: Elisha Owusu, Thomas Partey, Kwasi Sibo, Augustine Boakye, Caleb Yirenkyi, Abdul Fatawu, da Kamaldeen Sulemana.

'Yan Wasan Gaba: Christopher Bonsu Baah, Ernest Nuamah, Antoine Semenyo, Brandon Thomas-Asante, Prince Adu, Inaki Williams, da Jordan Ayew.

Rumbun Labarai
Scotland ta buga takardar kudi don murnar kwallon da McTominay ya ci, wadda ta kai su Kofin Duniya
Raphinha ya koka kan masu yawan cewa zai bar Barcelona
Iran ta ce dole Amurka ta ba da biza ga tawagarta ta Kofin Duniya ba tare da la'akari da siyasa ba
Karawar PSG da Bayern Munich za ta sake kayatarwa
Kungiyoyin Gasar Firimiya ta Ingila sun yi asarar dala biliyan 1 na kudin-shiga: Rahoto
Neymar ya yi dambe da ɗan Robinho a haduwarsu ta farko a filin atisaye na Santos
CAF ta tabbatar da ranakun gasar AFCON 2027 a Kenya, Tanzania da Uganda
Iran za ta buga wasannin Gasar Kwallon Kafa ta Duniya a Amurka duk da rikici, in ji FIFA
Tsohon ɗanwasan Nijeriya Eneramo ya mutu sakamakon bugun zuciya yayin wasan sada zumunta
Iran 'ba ta ƙarƙare yanke hukunci' kan halartar Kofin Duniya na 2026 a Amurka ba
Tottenham na neman masanin lafiyar tunani ga ‘yanwasanta, don gujewa fadowa daga gasar Firimiya
'Na yi imanin Arsenal ce za ta ɗaga Kofin Firimiya' - Arsene Wenger
Guardiola ya ce zai sallama Kofin Firimiya idan Man City ta sha kashi a hannun Arsenal
Nijeriya ta yi maraba da 'yarwasan tsere, Favour Ofili wadda aka hana ta sauya kasar da take wakilta
Shugaban FIFA ya ce akwai ‘tabbacin’ Iran za ta halarci Gasar Cin Kofin Duniya
Hukumar FA ta ci tarar Harry Maguire saboda rashin ɗa'a a wasan Man United da Bournemouth
UEFA ta yi watsi da korafin Barcelona kan wasan da Atletico Madrid ta doke su
Masoyin Arsenal ɗan Uganda na barazanar kai Gunners kotu kan damuwar da ya shiga bayan shan kaye
Danwasan Ghana, Kudus ya samu rauni a Tottenham, zai iya gaza zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026
Anthony Joshua 'zai koma damben boksin' bayan mummunan hatsarin mota