Lokaci na ƙarshe da nahiyar Arewacin Amurka ta karɓi baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta FIFA shi ne a 1994, lokacin da aka gudanar da gasar a Amurka.
Yayin da gasar ke dawowa nahiyar bayan shekaru 32, tana kuma alamta zango na ƙarshe ga manyan 'yan wasa biyu da ake ɗauka a matsayin mafi girma a tarihi, wato Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.
A cikin kusan shekaru 20 da suka gabata, fagen ƙwallon ƙafa na duniya ya kasance da wata fagen ɗanwasan Portugal, Christiano Ronaldo, da ɗan Argentina, Lionel Messi tamkar suna yin gasa ta kansu, yayin da sauran 'yanwasan duniya ke fafatawa a wata gasar daban.
Sun gina rayuwarsu ta ƙwallo mai ban al-ajabi, sun ci duk manyan kofuna, sun karya kusan dukkan tarihin bajinta da za a iya tunani, kuma sun ɗaga ƙungiyoyinsu zuwa matsayi da ba a taɓa gani ba.
Yanzu, yayin da suke shiga cikin ƙarshen rayuwarsu ta ƙwallo, Ronaldo mai shekaru 41 da Messi mai shekaru 39, za su jagoranci ƙasashensu na Portugal da Argentina, a gasar Kofin Duniya na FIFA 2026, a babin ƙarshe na aikinsu a matakin ƙasa-da-ƙasa.
Gwarzo mai dogon tarihi
An haifi Cristiano Ronaldo dos Santos Aveiro a garin Madeira na Portugal, inda ya fara buga ƙwallon ajin ƙwararru a kakar 2002-03 tare da Sporting CP ta Portugal.
Bayan wasan sada zumunci da ya ƙayatar tare da Manchester United ta Ingila, United ta ɗauko shi a 2004. Tare da United, ya lashe gasar Firimiya sau uku a jere, da kofin FA, da kuma Champions League a 2008.
A 2009, ya koma Real Madrid, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka fi samun nasara a ƙwallon ƙafa, inda tasirinsa a wasan ya fara bayyana.
Ronaldo ya ci komai da ake iya ci tare da Los Blancos, ciki har da La Liga, UEFA Champions League, Copa del Rey, da FIFA Club World Cup.
A 2018, ya kwashe shekaru uku a Juventus ta Italiya, inda ya samu kofunan Serie A biyu.
Bayan zamansa na biyu a Manchester United, Ronaldo ya koma kulob ɗin Al Nassr na Saudi Arabia, inda yake buga wasa zuwa yanzu.
Ronaldo ya bayyana a fili cewa 2026 tabbas za ta kasance gasar Kofin Duniya ta ƙarshe da zai halarta.
"(Kofin Duniya na 2026) tabbas zai kasance nawa na ƙarshe saboda zan kasance mai shekaru 41... Lokacin da nake cewa nan ba da jimawa ba [na yi ritaya], gaskiya nan ba da jimawa ba ne, saboda na ba da komai ga ƙwallon ƙafa.
“Na shafe shekaru 25 a wasan. Na yi komai. Ina da rakod da yawa. Ina matuƙar alfahari. Don haka mu more wannan lokaci, mu rayu a wannan lokaci," in ji Ronaldo ga CNN a wata tattaunawa a Nuwamban 2025.
Amma babban mai horar da Portugal, Roberto Martinez, ya nuna ƙarfin-gwiwarsa kan Ronaldo, yana cewa ɗanwasan mai ƙwarewa zai iya buga wani Kofin Duniya yana ɗan shekaru 45.
Lokacin da aka tambayi ko Ronaldo zai iya buga Kofin Duniya na 2030, Martinez ya faɗa kwanan baya ga gidan rediyon Cadena Ser, cewa "Bai kamata kowa ya yi shakku ba. Ya cancanci hakan."
Ronaldo yana halartar Kofin Duniya a karo na shida a tarihinsa, inda zai jagoranci Portugal a gasar ta bana. Portugal za su kasance masu masaukin baƙi tare da Spain da Morocco a gasar ta 2030.
Portugal za ta fara gasar bana da karawa da Congo DR ranar 17 ga Yuni, kafin su fafata da Uzbekistan ranar 23 ga Yuni. Wasansu na ƙarshe na Rukunin K zai kasance da Colombia ranar 27 ga Yuni.
A halin yanzu, Ronaldo ya sanar da fara 'ƙoƙarinsa' yayin da yake fara atisaye tare da tawagarsa.
Ɗanwasan ya wallafa a kafafen sada zumunta ranar Litinin, cewa "Começa a Missão Mundial!" ("Aikin Kofin Duniya Ya Fara!"), yana mai fatan lashe kofin duniyar ga ƙasarsa a bana.
Babban mai saita wasa
Yayin da ake girmama Ronaldo saboda kuzari, ƙwarewa wajen cin ƙwallaye, da iya tashi sama, an fi sanin Messi da gwanintar saita wasa da yin yanka.
Labarin Messi ya fara a Rosario, Argentina, inda aka haife shi a 1987, kafin daga bisani ya kwashe mafi rinjayen rayuwarsa ta ƙwallon ƙwararru a FC Barcelona.
Tare da Blaugrana, Messi ya kammala tattara rakodin ɗin lashe kofuna 35, ciki har da La Liga 10, Copa del Rey 7, Supercopa de España 8, Champions League 4, UEFA Super Cup 3, da FIFA Club World Cup 3.
A 2021, ya koma Paris Saint-Germain ta Faransa, inda ya samu ƙarin kofuna uku cikin shekaru biyu, ciki har da Ligue 1 sau biyu, da Trophée des Champions guda ɗaya.
A yanzu Messi yana buga wasa a Club Internacional de Fútbol Miami, wanda aka fi sani da Inter Miami, wani babban kulob a Amurka.
Messi ya bayyana cewa gasar 2026 kusan tabbas za ta kasance Kofin Duniya nasa na ƙarshe, alamar ƙarshen aikinsa a matakin ƙasa-da-ƙasa tare da tawagar Argentina.
"Kamar yadda na faɗa a baya, ban yi tsammanin zan buga wani ƙofin Duniya ba. A shekaruna, abin da ya dace shi ne tunanin ba zan yi ba," in ji tauraron na Argentina bayan nasarar tawagarsa ta 3-0 kan Venezuela a Satumban 2025.
A Disamban 2025, har ya amince cewa wataƙila ba zai buga gasar ta 2026 ba, duk da girman sha'awarsa ta halarta.
Sai dai Messi ya bar ƙofar a buɗe don yiwuwar wasannin sada zumunci a matsayin bankwana, amma sa-ran kafofin watsa labarai, da abokan wasa, da ƙungiyar ƙwallo ta Argentina suke da shi, shi ne zai yi ritaya daga wasan ƙasa-da-ƙasa bayan kammala Kofin Duniya.
A Inter Miami, bai yi ritaya ba tukuna, saboda ma ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi har zuwa kakar 2028.
Messi da Ronaldo: haɗin da ba shi da tamka
Yawancin masu sharhi kan ƙwallon ƙafa sun yarda cewa babu wanda ya kusanci matakin da waɗannan 'yan wasan biyu suka kai.
Hakan ya haɗa da matasan taurari kamar Erling Haaland na Norway, da Kylian Mbappé na Faransa, har ma da tsofaffin taurari da suka taka leda tare da Ronaldo da Messi, ciki har da Neymar na Brazil, Luis Suárez na Uruguay, Karim Benzema na Faransa, Mohamed Salah na Masar, da Robert Lewandowski na Poland.
Ronaldo, har yanzu, shi ne mafi yawan ƙwallaye a tarihin ƙwallon ƙafa, tare da ƙwallaye sama da 970, kuma har yana neman kai wa gaƙwallo 1,000 kafin ya daina wasa.
Idan aka karkasa bisa matakin gasa, lambobinsa har yanzu suna da wahalar cimmawa.
Ronaldo, wanda ake wa kirari da "Shagon Champions League", ya zura ƙwallaye 450 ga Real Madrid, 145 ga Manchester United, 101 ga Juventus, da fiye da 100 ga Al Nassr.
A halin yanzu shi ne mafi yawan ƙwallaye a tarihin UEFA Champions League da ƙwallo 140. Haka kuma shi ne mafi yawan ƙwallaye a tarihin wasannin ƙasa-da-ƙasa na maza, da ƙwallo 143, sai kuma Messi mai ƙwallo 116, sannan Ali Daei na Iran da ƙwallo 108.
A gefe guda, Messi shi ne ɗanwasan da ya fi samun kofuna a tarihin ƙwallon ƙafa, da rakod ɗin kofuna 46, sai tsohon abokin aikinsa a Barca, Dani Alves da kofi 43, sai Hossam Ashour na Masar da kofi 39.
Messi ya ci kusan ƙwallaye 800 a tsawon wasanninsa na matakin ƙwararru.
Ya zura ƙwallo 672 ga Barcelona, 35 ga PSG, da 67 ga Inter Miami, kuma adadin yana ci gaba da ƙaruwa.
Zai zama babban ƙalubale ga 'yanwasa kamar Mbappé da Haaland su nemi kamowa ko wuce waɗannan adadi.
Takara ta ƙarshe
A gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026, magoya baya a duk duniya za su saka ido sosai kan waɗannan jarumai biyu yayin da suke fafatawa a gasarsu ta duniya ta ƙarshe.
Wannan zai zama wani rakod saboda shi ne karo na shida a gasar Kofin Duniya ga kowannensu.
Messi ya buga a gasar ta 2006, 2010, 2014, da 2018, kuma ya lashe Kofin a 2022.
Ronaldo ya buga a 2006, 2010, 2014, 2018, da 2022. Bai taɓa lashe Kofin Duniya ba, don haka wannan shi ne damarsa ta ƙarshe da zai iya ɗaukar wannan ƙofin da ya daɗe yana nema.
Akwai ma yiwuwar cewa taurari biyun za su haɗu a filin wasa a ranar 11 ga Yuli a Kansas City, a wasan zagayen kwatafainal, idan Argentina ta iya kaucewa "bakin da yake bin zakarun bara su kasa taɓuak komai", da kuma Portugal idan sun ci nasara a rukuninsu.
Ko da yake duka taurarin sun buga kowace gasar tun 2006, Argentina da Portugal ba su taɓa cin karo a gasar ba.
Wannan zai iya zama karo na farko kuma na ƙarshe, kuma zai zama abin da zai kasance babban nishadi ga magoya baya, ganin Messi da Ronaldo suna fafatawa a wannan rawa tasu ta ƙarshe.












![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=512&format=webp&quality=80)
