Ana hasashen cewa Musulmai za su zarta Kiristoci wajen yawan jama'a a duniya nan da shekarar 2035, kamar yadda wani sabon hasashen cibiyar Bincike ta Pew Research Center kan makomar addinai a duniya ya nuna.
Rahoton, wanda ya yi nazari kan yadda mabiya addinai bakwai za su bunƙasa tsakanin shekarar 2020 zuwa 2070, ya gano cewa addinan biyu na ƙara samun mabiya, amma Musulmai na ƙaruwa cikin sauri fiye da Kiristoci.
Rahoton ya ce idan aka ci gaba da samun irin wannan yanayi, adadin Musulmai a duniya zai haura biliyan 3.6, yayin da Kiristoci za su kasance ƙasa da biliyan 3 nan da shekarar 2070.
Ana hasashen cewa yawan al'ummar duniya baki ɗaya zai ƙaru da kashi 29 cikin 100 a wannan lokaci. Musulunci da Kiristanci ne kaɗai ake hasashen cewa yawan mabiyansu zai ƙaru daidai da wannan bunƙasar ko fiye da ita, inda ake sa ran Kiristoci za su ƙaru da kashi 30 cikin 100, yayin da Musulmai za su ƙaru da kashi 80 cikin 100.
A cewar rahoton, Musulmai za su kasance kashi 36 cikin 100 na al'ummar duniya nan da shekarar 2070, idan aka kwatanta da kashi 26 cikin 100 a shekarar 2020. Yayin da adadin Kiristoci zai ci gaba da kasancewa kashi 29 cikin 100.
Cibiyar Pew ta danganta wannan sauyi da dalilan da suka shafi tsarin haihuwa da shekarun al'umma. Rahoton ya nuna cewa tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025, matsakaitan yaran da mace Musulma take haihuwa shi ne 3.1, idan aka kwatanta da yara 2.0 ga matan da ba Musulmai ba.
Haka kuma, matsakaicin shekarun Musulmai a shekarar 2020 ya kasance 24, kusan shekaru goma ƙasa da na waɗanda ba Musulmai ba, wanda yake shekara 33.
Ana kuma hasashen cewa mafi yawan ƙarin yawan al'ummar duniya a wannan ƙarni zai kasance ne a yankin Afirka kudu da hamadar Sahara, inda mafi yawan al'ummar yankin mabiya addinin Kiristanci ne ko Musulunci.
Rahoton ya kuma yi hasashen cewa nan da shekarar 2070, Pakistan za ta kasance ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan Musulmai a duniya, sai Indiya, da Nijeriya da Indonesiya.
Haka kuma, ana sa ran Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo za ta zarta Amurka wajen yawan Kiristoci.
A gefe guda kuma, ana hasashen cewa Amurka, Canada da Jamus ba za su kasance cikin ƙasashen da ke da yawan Kiristoci ba nan da shekarar 2070.
Rahoton ya kuma nuna cewa yawan mabiya addinin Hindu da Yahudanci zai ƙaru, amma kasonsu cikin al'ummar duniya zai ragu. Yayin da ake hasashen cewa yawan mabiya addinin Buddah zai ragu, tare da raguwar kasonsu a duniya.
Sai dai rahoton ya bayyana cewa hasashen ya dogara ne kan zato cewa yanayin sauya addini da ƙaura daga wata ƙasa zuwa wata zai ci gaba da kasancewa kamar yadda yake a baya bayan nan.
Pew ta ce hanyar da ta bi na iya zama ta yi la’akari da mafi ƙarancin adadi dangane da ƙaruwar masu danganta kansu da addinai, kasancewar adadin mutanen ya ƙaru da sauri fiye da yadda aka yi hasashe tsakanin shekarun 2010 da 2020.























