| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Zaben FIFA: Philippe Diallo na Faransa zai kara da Infantino bayan samun goyon bayan UEFA da Macron
Bayan samun goyon bayan shugaban Faransa, Emmanuel Macron, Diallo na neman haɗa-gwiwa da wani sabon ɗan takarar, Kozo Tashima daga Japan.
Zaben FIFA: Philippe Diallo na Faransa zai kara da Infantino bayan samun goyon bayan UEFA da Macron
Philippe Diallo shi ne shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Faransa, FFF / AFP (Wire)

Ɗan takarar shugabancin Hukumar Ƙwallo ta Duniya, FIFA, Philippe Diallo ya bayyana cewa shugaban Faransa Emmanuel Macron yana bayansa, yayin da ya fara fafutukar karawa da shugaban FIFA na yanzu, Gianni Infantino.

Shigowar Diallo takarar na zuwa ne a ƙurrerren lokaci, bayan da tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger, wanda shi ma Bafaranshe ne ya ƙi amincewa ya shiga takara don kawar da Infantino.

Diallo, wanda shi ne shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Faransa, FFF, ya ce zai nemi haɗa hannu da wani sabon ɗantakara daga Japan, Kozo Tashima, wanda mamba ne a kwamitin FIFA kuma tsohon shugaban hukumar ƙwallo ta Japan.

Ranar Talata, 17 ga Nuwamba, Diallo ya tabbatar da cewa zai nemi taimakon Tashima don kaucewa rarraba ƙuri’un masu adawa da Infantino.

“Idan muna so mu yi nasara, na yi imanin dole mu haɗa ƙarfi da ƙarfe,”in ji Diallo yayin wata zantawa da ‘yanjarida a Paris.

Mai shekaru 63, Philippe Diallo ya ce bai yi niyyar shiga takarar ba, amma kwamitin zartarwar hukumar ƙwallo ta Turai, UEFA ne ya nemi ya tsaya ranar Litinin, kuma hukumar ƙwallo ta Faransa ta amince da murya ɗaya.

Damar kayar da Infantino

Gianni Infantino ya yi baƙin jini a duniyar ƙwallo sakamakon jerin batutuwa da suka shafi yadda yake gudanar da harkokin ƙwallo, ciki har da ƙirƙirar kyautar FIFA ta zaman lafiya, wadda ya bai wa Shugaba Donald Trump na Amurka a 2025.

Haka nan an zargi Infantino da yin katsalandan wajen ɗage dakatarwar da aka yi wa ɗanwasan tawagar Amurka, Folarin Balogun, yayin gasar Kofin Duniya bayan Trump ya kira shi a waya.

A watan Yulin da ya gabata, Infantino ya fasa wani shirinsa na na sayar da hannun jarin kashi 20% na kamfanin kasuwanci na FIFA, wanda ya kai dala miliyan $4.2, wato FIFA Forward Enterprise, wanda shi ne batun da ya haifar da bore daga ƙasashen Turai.

Infantino na shirin neman wa’adi na huɗu na shugabancin FIFA, kuma yana da goyon baya daga hukumomin ƙwallo na Afirka, CAF, da na Kudancin Amurka, CONMEBOL.

Masu sharhi kan zaɓen FIFA sun gaya wa Reuters cewa duk da hukumar UEFA tana da ƙuri’u ​55 daga cikin jimillar ƙuri’u ⁠211 na zaɓen FIFA, Diallo ba shi da goyon bayan duka ƙasashen Turai.

Ranar Larabar nan ne za a rufe karɓar ‘yantakarar shugabancin FIFA, kafin a tantance su zuwa ranar 18 ga Fabrairun baɗi. Zaɓen zai gudana a birnin Rabat na Maroko, ranar 18 ga Maris ɗin 2027.