| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya na gaf da samar da ‘yansandan jiha yayin da majalisun jihohi 36 suka amince da shirin
Nijeriya na kara matsawa kusa da ba wa jihohi karfin kula da ‘yansanda bayan jihohi 36 sun amince da gyaran kundin tsarin mulki da ke ba wa jihohi damar kafa ‘yansandansu tare da na tarayya.
Nijeriya na gaf da samar da ‘yansandan jiha yayin da majalisun jihohi 36 suka amince da shirin
Kudirin gyaran kundin tsarin mulkin na neman samar da tsarin doka da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yan sandansu. / AP (Wire)

Magatakardar Majalisar Dokokin Ƙasa, Kamoru Ogunlana, ya sanar da amincewar da aka cim ma baki ɗaya a ranar Litinin, inda ya ce adadin ya zarce ƙa’idar kundin tsarin mulkin ƙasar da ke buƙatar amincewar aƙalla jihohi 24.

Ya ce an kammala tantance sahihancin ƙudurorin, kuma an shirya tura kudirin ga Shugaba Bola Tinubu domin ya sanya masa hannu.

Kudirin gyaran kundin tsarin mulkin na neman samar da tsarin doka da zai bai wa jihohi damar kafa rundunonin ’yan sandansu tare da gudanar da ayyukansu da kansu.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar rashin tsaro ke ƙaruwa a sassan Najeriya, ciki har da satar mutane domin neman kuɗin fansa, ayyukan ’yan bindiga, hare-haren makamai da rikice-rikicen al’umma.

Masu goyon bayan matakin sun ce kafa rundunar ’yan sandan jihohi zai inganta tattara bayanan sirri, ƙarfafa aikin tabbatar da tsaro a cikin al’umma, tare da ba da damar gaggauta mayar da martani ga barazanar tsaro.

Sai dai masu suka sun nuna damuwarsu kan yiwuwar gwamnonin jihohi su yi amfani da rundunonin ’yan sandan wajen cim ma muradun siyasa, baya ga batutuwan samar da kuɗaɗe, ƙa’idojin ɗaukar ma’aikata, bin diddigi da ɗora alhaki, da kuma haɗin gwiwa da rundunar ’yansandan tarayya.

Sun yi kira da a samar da tsauraran matakan kariya a kundin tsarin mulki domin tabbatar da cewa rundunonin ’yansandan jihohi za su gudanar da ayyukansu bisa ƙwarewa da kuma ’yancin kai, ba tare da katsalandan na siyasa ba.